– Anotonio Guterres ne sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya
– Guterres zai maye gurbin Ban-ki Mon wanda wa’adin sa ke karewa
– Sabon Shugaban Zai hau kujera wata mai zuwa
An nada sabon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya
Majalisar Dinkin Duniya
ta samu sabon Shugaba wanda zai maye gurbin Shugaba Ban-Ki Mon yayin da wa’adin
sa ya cika. Ban-Ki Mon zai sauka daga kujerar ne Ranar farkon shekara mai zuwa.
Antonio Guterres tsohon
Firayim Ministan Kasar Portugal ne na Kasar Turai, ya kuma rantse cewa idan ya
hau zai yi gaskiya. Tsohon Firayim Ministan yayi alkawarin bin dokoki da
muradun Majalisar Dinkin Duniya yayin da ya dare Shugabanci.
Shekaran Jiya ne
Jaridar Premium Times tace an gama shirin nada Ministar Kasar nan, Amina
Mohammed a matsayin Mataimakiyar Shugabar Majalisar Dinkin Duniyan, kuma nan da
wani dan lokaci za a sanar. Sai dai har yanzu ba a samu wani bayani ba. Fadar
Shugaban Kasa dai tace ba ta san wannan maganar ba.
Sabon Sabon Shugaban Majalisar Dinkin
Duniyan, Antonio Guterres yace zai kawo gyara a Majalisar. Antonio Guterres yace
dole a ga canji.
No comments:
Post a Comment