A
Kasar Egypt za a fara kama masu yi wa mata kaciya
– Kasar Masar za ta dauki mataki mai tsanani ga masu yi wa ‘ya ‘ya mata kaciya
– Za a daure duk wanda aka kama na shekaru 15 kamar yadda Majalisa ta amince
– Za a rika lura da kowane Asibiti ganin an hana kaciya ta mata
A Kasar Egypt, yanzu an kafa
doka mai tsanani ga duk wanda aka kama yayi wa diya mace kaciya. Sabuwar dokar
da aka sanya kwanan nan za ta sa a daure mutum na shekaru da dama a gidan kaso
idan aka kama sa da laifi.
Kasar Egypt din dai tayi
garambawul ga dokokin Kasar inda yanzu za a iya jefa mutum yari na shekaru 15
idan har aka kama sa da laifin yi wa yara mata kaciya. A Ranar Talata da ta
wuce ne dai Majalisar Kasar ta saka hannu kan wannan doka.
Ma’aikatar Lafiya ta bada
sanarwar cewa daga yanzu, Gwamnati za ta rika bibiyar duk Asibitocin Kasar
ganin an kawo karshen kaciya da ake yi wa mata, watau abin da ake kira FGM. Ko a
baya dai an taba kame wani Likita bayan da yayi wa wata yarinya kaciya.
An saba yi wa mata kaciya
musamman a Kasashe irin su Masar, wasu na ganin dai hakan yana da illa ga ‘ya
mace. Sai dai yanzu an fara samun sauki Inji Hukumar UNDP.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment