– Nnamdi Kanu yace idan ya bude baki yayi magana sai Najeriya ta wargaje
– Ana nan ana ta shari’ar Nnamdi Kanu
– Kotu tace ba za ta sake Kanu ba, don kuwa laifin sa ba na wasa bane
Wata sabuwa: Shugaban
Kungiyar ‘Indigenous People of Biafra’
Watau (IPOB) ta Biafra Nnamdi Kanu, yace zai rikita Najeriya kuma mai gidan
Rediyon Biafra yace idan har yayi magana fa Kasar nan za ta watse.
Ana nan dai ana ta shari’ar Nnamdi Kanu, wanda yake rike
tun bara. Kotu tace ba zai yiwu hakanan ta bada belin Kanu ba don kuwa akwai
abin ba na wasa bane. Alkali mai shari’a Nyako tace ba za ta saki Nnamdi Kanu
da sauran wadanda ake kara ba. Nnamdi Kanu yace kokari ake yi a ga bayan sa,
kamar yadda aka kashe mutanen su a Kasar Ibo.
Babban Kotun Tarayya da ke Abuja tace za ta bada damar a
fara bada shaida kan karar amma ba tare da an ga masu bada shaidar ba. Sai dai
Kanu da Lauyoyin sa sun ce ba za si yarda da wannan ba ko kadan.
Kanu yace da Kotu Buhari na kokarin ganin bayan sa ne
kurum. Har sai da ta kai Lauyan na sa, Lauya Chucks Mouma SAN ya roke sa da
yayi shiru a Kotun. Kanu yace idan ya bude baki Najeriya za ta tashi.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment