NEMAN HALAL A DUNIYA DOMIN LAHIRA
Hudubar Jumu’a daga Masallacin I.T.N Zangon-Shanu, Zaria
Daga Bakin Sheikh Salihu S. Abubakar
BismilLahir Rahmanir Rahim.
Dukkan Godiya ta
tabbata ga Allah, Shine wanda ya kammala mana addinin mu, kuma ya cika mana
ni’momi. Muna godiya da yabo gare Shi Madaukakin Sarki, Shine yayi mana wata
babbar baiwa ta hanyar aiko da Mafificin ta’likai duka-Shugaban mu, Annabi
Muhammad SAW. Muna shaidawa cewa lallai babu abin bautawa da gaskiya face
Allah, shi kadai ya ke, ba shi da abokin tarayya. Shi kuma Allah, yayi alkawari
ga masu tsoron sa cewa zai saka su cikin Gidan Aljanna-Gida na Aminci. Muna
shaidawa lallai Shugaban mu, Annabi Muhammad SAW Bawan Allah ne, kuma Manzon
sa, wanda yake mai Madaukakin daraja da kuma mafi daukaka na mukami.
Bayan haka:
Ya ku ‘Yan uwa,
lallai Allah SWT, tsarki ya tabbata gare sa tare da daukaka, ya fadi a cikin
Littafin sa mai girma. Allah SWT yace: ‘Lallai,
Hakika, A gare ku akwai kyakkawan abin koyi a cikin tafarkin Annabi Muhammad
SAW, ga duk wanda yake fatan samun yardar Rahamar Allah da kuma Ranar
Lahira...’ Saboda haka, babu makawa gare mu, lallai ne mu yi duk abin da za
mu iya saboda mu yi koyi da irin halayen sa da dabi’un Sa, Shi Manzon Allah
SAW. Shi ne abin koyi, Shi ne jagora da ya kamata mu bi. Kuma babu lokacin da
muka fi bukata muyi koyi, kuma mu siffantu da dabi’un sa kamar wannan lokaci da
muke ciki. Shi SAW ne ya karantar da mu abin da wannan Duniya ta ke ciki gaba
daya. Shi SAW ne ya fada mana cewa Duniyar nan Halittar Allah ce, kuma Allah ya
kawo mu wannan Duniya domin jarrabawa, kuma za mu koma gare sa. Shi SAW ne ya
mana bayanin menene manufa a cikin wannan rayuwa ta duniya, Shi ne yayi mana
bayanin tafarkin da ya kamata mu bi a cikin rayuwar mu ta Duniya. Saboda haka,
duk wanda yayi koyi da irin shiriyar Sa ya rabota, ya kuma yi nasara. Wanda
kuma ya aikata sabanin haka, ya bata, kuma ya halaka.
Shi Annabin mu, SAW
ya karantar da mu cewa ita rayuwar Duniya tana da Manufofi wadanda suke guda 2.
Manufar farko ita ce Bautar Allah, sannan manufa ta biyu ita ce mu rayar da
wannan samuwa watau mu raya wannan Duniya baki daya. Ko da yake wannan manufa
ta biyu, bangare ne na wancan na farko. Ma’ana; aikin da za muyi wajen raya
duniya, duk wani bangare ne na Aikin Bautar da Allah SWT ya wajabta mana. Allah
ya fada cikin Al-Kurani cewa: ‘Ban
halicci mutane da Aljani ba, sai don su bauta mani’. Kuma shi Allah
Madaukaki SWT ne yace; shi ne wanda ya tsirar da halittar ku daga cikin Kasa,
kuma ya sa ku raya ta. Watau ku za ku raya ta, ku gyara ta, ita Duniya.
Allah SWT ya umarci
Dan Adam yayi riko da sababi a cikin rayuwa, wanda za su zama daukaka ga
Al’ummar mu da kuma gyara rayuwar mu ta duniya domin ta zama matakala zuwa
Lahira. Kuma wannan Addinin na mu kamar
yadda Manzon mu Annabi Muhammad SAW ya karantar da mu, ya hana mu shantakewa da
lalaci da ragwanci. Saboda ba zai yiwu ba a cin ma abin da Allah yake so a ban
Kasa da lalaci da kuma ragwanci. Allah Madaukakin Sarki ya fada mana cewa: ‘Shi Allah ne wanda ya sanya Kasa ta zama
horarriya, saboda haka, kuyi ta yawatawa cikin sasannin ta, kuma ku ci daga
cikin arzikin Allah, kuma gare sa za ku taru.’
Saboda haka
Musulunci ya karantar da duk abin da ake bukata wajen rayar da Duniya, ta
wannan hanyar ne kuma za a samu gina lahira. Musulunci ya kuwa kwadaitar da
cewa a yawata a cikin Kasa, a zurfafa cikin sasannin Kasar wajen samun arziki
mai albarka wanda yake cikin tudu da kuma ruwa. Tare da kuma karfafa gwiwa da
Musulunci yayi a kan a tashi ayi aiki tukuru, ya zo a cikin Hadisin da Miqdam
ya ruwaito cewa: Annabi SAW yace: ‘Babu
wani abinci da daya daga cikin ku zai ci, da ya fi abin da mutum ya aikata da
hannun sa, ya samo...’ Sai Annabi SAW ya cika da cewa kuma Lallai Annabi
Dawud AS, ya kasance yana ci ne daga aikin hannun sa.
[Imamul Bukhari ya kawo
wannan Hadisi.]
Saboda haka shi
Musulunci, wanda Manzon Allah SAW ya zo mana da shi, kira ne baro-baro da cewa
duk wanda ya yarda da Musulunci ya tashi yayi aiki tukuru domin tabbatar da
Duniya da raya ta, ta yadda za a jawo Alheri ga dukkan Duniya. Shi Musulunci ya
girmama al’amarin aiki tukuru, ya kuma sa hakan ya zama hanya da zai kai mutane
ga cigaba da daukaka a nan duniya, kuma ya zama ibada.
Ayoyin Qur’ani sun
kwadaitar da karfafa gwiwa wajen tashi da yin aiki tukuru a wajen al’amarin
rayuwa da kuma abin da zai kawo abinci da tufafi da sauran bukatu na mutum da
iyalan sa. Saboda haka ne Allah SWT yayi umarni da Sallar Jumu’a, bayan Sallar
kuma yayi umarnin a bazu cikin Kasa domin a nema daga cikin falalar Allah.
Allah Madaukakin Sarki yace: ‘Idan an
gama Sallar Jumu’a, ku bazu a cikin Kasa, ku nema daga cikin Rahamar Allah,
amma ku rika tuna Allah ko ku samu babban rabo.’ Wannan umarni ne Allah,
kamar yadda aka yi umarni da azo Masallaci ayi Sallar Jumu’a, haka aka yi
umarni da a yadu a ban Kasa, a nema daga cikin falalar Allah bayan an tashi
daga Masallacin.
Hakika wannan
Addini na mu na Musulunci yayi mana bayani cewa duk wanda yayi ta kokari domin
neman abincin sa da na ‘ya ‘yan sa ta hanyar halal, yana daidai da darajar
wanda ya mutu shahidi a wajen yaki ko kuma wanda aka sa gadi ya tare kofofin da
abokan gaba za su kawo hari. Saboda haka, yana daya daga cikin wadanda suka yi
aiki ta hanyar daukaka kalmar Allah. Akwai Hadisi daga Ka’ab Dan Ujrah RA yace;
Wani mutum ya wuce ta gaban Manzon Allah, sai Sahabbai suka ga irin kirar jikin
sa da kuma kuzarin sa, wannan abu ya ba su sha’awa, sai suka ce da RasululLah
SAW cewa dama ace wannan mutumi yayi amfani da kuzarin sa cikin tafarkin Allah.
Sai Manzon Allah SAW yace ai in dai yana kokari ne domin nemawa kan sa da
iyalin sa; kananan yara, abinci ne, to yayi cikin tafarkin Allah. Yace idan
kuma ya fita ne domin samun abin da Mahaifan sa-da suka tsufa za su ci, shi ma
duk cikin Tafarkin Allah ne. Manzon Allah SAW yace idan har ya fito ne domin
samun abin da zai ci, ya kare kan sa daga fadawa sharri, to wannan duk cikin
tafarkin Allah ne. Amma idan ya fito ne domin ya samu abin da zai yi alfahari
da shi, ko ya tara arziki, to wannan yana cikin Tafarkin Shaidan. Imamul Tabarani
ya fito da wannan Hadisi.
Shi kuma Musulunci
bai ma tsaya ga karfafa mana gwiwa kawai ba, ya kuma neme mu da muyi aiki da
kyau; babu magudi da ha’inci. Wannan shi ne abin da Manzon Allah SAW ya koyar
da mu-kyautata aiki. Wannan saboda mu samu soyayyar Allah da kuma Rahamar sa.
An sami Hadisi daga Aisha RA tace: Manzon Allah yace: Lallai Allah mai girma SWT yana so idan mutum zai yi wani aiki, ya
tsaya yayi sa za-kyau. Allah SWT da kan sa yana fada mana cewa: Ku kyautata domin Allah yana son masu kyautatawa.
‘Yan uwa ina so ku
rike wannan daga cikin Hudubar; Idan za mu rike Addinin mu da kyau, mu rika
biyayya kuma mu tashi muyi aiki tukuru; don babu wani aiki na Duniya-wanda yake
dabam da na Lahira, wannan ba karantawar Addinin Musulunci bane. Kowane aikin
Duniya, ana yin sa ne domin neman Lahira, ko da a zahiri za mu ga cewa an ci
moriya a Duniya, ana aikin ne domin Lahira. Duk wanda ya dauka cewa akwai wani
aikin neman Duniya da kuma na Lahira, bai fahimci Addinin Musulunci ba. Wane
lokaci ne na Allah, wane lokaci ne kuma na mutum? Duk lokacin ka na Allah SWT
ne; daga kasuwanci, aikin Gwamnati, zuwa noma dsr. Duk aikin da mutum yake yi,
idan har ka tsaya kayi aiki yadda Allah yace, to wannan aikin ibada ne kuma zai
ba mutum matsayin shahidi, haka wannan lamari yake. Saboda haka, ya kamata kowa
ya fahimci wannan, muddin muka fahimci wannan, za mu gina rayuwa mai kyau a nan
Duniya da kuma Lahira.
Allah ya bamu
fahimtar AlQurani mai Girma, ya amfane mu gaba daya da abin da ke cikin sa na
Ayoyi masu wa’azi da hikima. Allah ya tserar da mu daga Azabar sa mai radadi.
Allah kayi dadin tsira ga Annabin Ka SAW da iyalan sa kamar yadda ka yi dadin
tsira ga Sahabban Manzon Allah SAW da wadanda suka bi bayan su bisa tafarki
madaidaici. Allah ka kama hannuwan wadanda ka Shugabantar da su a matakai
dabam-dabam zuwa ga abin da kake so ka yarda shi.
Muhammad
Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Zaria.
No comments:
Post a Comment