– Dan Majalisar nan, Hon. Gudaji Kazaure yace bai dace Gwamnati ta hana shigo da motoci ta iyakar Kasa ba
– Gudaji Kazaure yace wannan ya sabawa ka’idar
Damukaradiyya gaba daya
– Daga karshen watan nan, babu
damar shigo da motoci kowace iri sai ta iyakar teku
Kwastam ta han shigo da motoci: Gudaji Kazaure yace sam ba za ta yiwu ba..
Kwanan nan ne Gwamnatin
Tarayyar Najeriya ta bada umarnin hana shigo da motoci fadin Kasar nan ta
iyakar Kasa. Gwamnatin Kasar dai tace haramcin ya shafi sababbi da tsofaffin
motoci zuwa cikin Kasar ta Najeriya kamar yadda Hukumar Kwastam ta sanar.
Sai dai Dan Majalisar nan
mai wakiltar Yankin Jihar Jigawa yace hakan ya sabawa Damukaradiyya idan dai da
gaske Gwamnatin ta Jama’a ce. Gudaji Kazaure yace mutane da dama ba su da halin
sayen sababbin motoci daga Kasar Amurka da Japan.
Gudaji Kazaure ya bayyana
bacin ran sa ne a Majalisa, yace idan aka kyale to jama’a da dama, musamman na
Arewa za su rasa aikin yi. Dan Majalisan yace masu shigo da motoci ta Cotonou
su kan biya kudin da doka ta sa a iyakar Jibia da Seme da ke Legas da Katsina.
Hukumar Kwastam dai tace
daga Junairun shekara mai zuwa, babu damar shigo da motoci ta kan iyakar Kasa.
Za a bari ne a rika shigo da motoci kawai ta iyakar ruwa.
No comments:
Post a Comment