Monday, December 12, 2016

Wani Gwamna ya tsallake rijiya da baya

– Wani Coci ya rushe a Akwa-Ibom inda da dama suka hallaka a sanadiyar haka

 

– Shugaba Muhammadu Buhari  ya aika ta’aziyar sa ga wadanda abin ya shafa

 

– Shugaban Kasan ya kira Gwamna bayan abin ya faru

 

 
Coci ya rushe a Akwa-Ibom, da dama sun hallaka

 

Wani Coci ya rushe a Akwa-Ibom, wanda hakan yayi sanadiyar rasa rayukar daruruwan mutane. Wannan abu dai ya faru ne a Babban Birnin Akwa-Ibom, Uyo. Gwamnan Jihar, Udo Emmanuel ya tsallake rijiya da baya shi ma. 

Shugaba Buhari ya mika ta’aziyar sa ga wadanda abin ya auka da iyalan su. Mutane fiye da 100 ne dai suka rasa rayukan su. Jaridar Premium Times tace ginin Cocin gaba daya ya zube Kasa war-was. 

Gwamnan Jihar yana cikin wadanda ke cikin Cocin, sai dai daf da abin zai faru ya fita. Amma mutane da dama, ba su taki wannan sa’a ba. Rahotanni sun nuna cewa yanzu Sakataren Gwamnatin Jihar Akwa-Ibom da kuma Sakataren yada labarai suna asibiti kwance. 

Shugaba Buhari ta bakin Garba Shehu yace Shugaban Kasa ya kira Gwamna Emmanuel ta wayar tarho, inda ya masa murnar tsira da rayuwar sa, ya kuma jajanta masa abin da ya faru a Jihar sa.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...