Tuesday, November 29, 2016

Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da Fidel Castro


– Tsohon Shugaban Cuba Fidel Castro ya bar duniya Ranar Jumu’a

 

Fidel Castro ya rasu yana da shekaru 90

 

Tsohon Shugaban ne ya jagoranci juyin juya-halin da aka yi a Kasar Cuba shekaru 50 da suka wuce

 

Shin Wanene Fidel Castro?

 

 Castro kenan yana busa karar sa 'yar gida

Yayin da ake zaman makokin Fidel Castro a Kasar Cuba. Mun kawo maku dan takaitaccen Tarihin sa.

  •  An haifi Fidel Castro a shekarar 1926, a Garin Oreiente da ke Yammacin Kasar Cuba

  • An daure Fidel Castro a shekarar 1953 bayan yayi yunkurin kifar da Gwamnati

  • A shekarar 1955 aka saki Fidel Castro daga Gidan Yari

  • A shekarar 1959 ya samu kifar da Gwamnatin Shugaban Kasar lokacin, ya zama Shugaba

  • A shekarar 1961 ya yaki harin da wata Kungiya da CIA ta Amurka ta marawa baya ta kawo masa
  •  
  •  A shekarar 1976 Majalisar Kasar Cuba ta zabi Fidel Castro a matsayin Shugaban Kasa

  • A kuma shekarar 1976 ya kulla yarjejeniya da Kasar Amurka  game da ‘Yan gudun Hijira

  •  A shekarar 2006 ya sauka daga Shugabancin Kasar Cuba 

  • Dan uwan sa Raul Castro ya gaje sa
  •  
  • Fidel Castro ya mutu a shekarar 2016 yana mai shekaru 90 a duniya. 

[BBC]




No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...