Friday, December 23, 2016

2019: Jonathan zai tsaya takara?


– Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya kawar da kura game da batun tsayawan sa takara mai zuwa


– Ana ta yada cewa Tsohon Shugaban na shirin kara dawowa


Goodluck Jonathan yace duk zancen banza ne na mutane




Tsohon Shugaban Najeriya, Dr. Goodluck Jonathan ya musanya labaran da ke yawo na cewa zai kara tsayawa takarar Shugabancin Kasar nan. Jaridar The Nation ta rahoto Shugaban yana karyata jita-jitan da ake ji.

Shugaba Jonathan yayi jawabi ne ta kafafen yada labarai inda ya kira labaran da sunan kirkirar mutane. A baya an ce Jonathan ya gana da mutanen sa domin ganin yadda zai dawo mulki. Yace karya ne don a lokacin ma ba ya gida, sai kwanan nan ya dawo domin kiresmeti.

Tsohon Shugaba Jonathan Goodluck dai yayi abin da ba a taba yi ba a Kasar nan. A zaben Kasar da ya wuce Shugaban ya sha kashi lokacin yana kan mulki a hannun Jam’iyyar adawa. Salin-alin Shugaban ya tattara ya bar mulkin ba tare da wani jayayya ba.

Tsohon Shugaban Kasar ya sha fada cewa bai dace a zubar da jinin ko mutum daya ba a Kasar saboda manufar sa shi daya, don haka ne ya sauka daga mulki. Jonathan di yayi wa masu bikin Kiresmeti fatan alheri.

[NAIJ Hausa]


No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...