Jami’in
Dan Sanda yayi fada da Direban mota...ya rasa Bindiga
– An ga wani Dan Sanda yana fada da
Direba a Legas
– Jami’in ya rasa Bindigar sa wajen
kokarin karbar N500
– Wannan
abu ya faru ne a Ikorodu ta Legas
An ga wani Dan Sanda yana
fada da wasu mutane uku a Unguwar Ikorodu ta Jihar Legas. An dauki hoton wannan
Jami’i ne yayin da rikici ya rincabe tsakanin sa da wani Direban mota a wurin.
A dalilin haka ne ma Dan
Sandan ya rasa Bindigar sa wajen kokawa da mutanen. An ji wani daga ciki yana
kiran a dauki Dan Sandan hoto, don kuwa ta shi ta kare idan aka yi haka. Hakan
dai kuwa aka yi.
Saboda dai cin hancin N500
ta kai wannan Dan Sanda ya rasa bindigar sa. Kamar yadda The Punch ta bada
labarin bidiyon da aka yada. An ga Dan Sandan yana kokarin karbar cin hancinn
N500 daga hannun Direban wata babbar mota.
A Garin Zariya kuma, Jiya da
safe, an samu takaddama tsakanin Soja da wani Jami’in tsaron, har ta kai wannan
Jami’in nan Mobile Police ya shiga buda wuta babu dalili a gaban wani Bankin
Zenith da ke Unguwar PZ.
No comments:
Post a Comment