– Gwamnatin Jihar Kaduna ta haramta tattaki a fadin Jihar
– Gwamnati tace daga yanzu babu wani taro na gaira-babu dalili
– Ana hakan ne domin a kawo karshen ‘Yan kungiyar IMN na Shi’a a Jihar
Gwamnatin
Jihar Kaduna ta bayyana cewa daga yanzu babu wani tattaki ko gangamin da ya sabawa doka a Jihar.
Gwamnatin tayi wannan ne domin kawo karshen lamarin ‘Yan Kungiyar IMN na Shi’a a Yankin.
Mai magana da bakin Gwamnan Jihar Nasir El-Rufai, Samuel
Aruwan ne ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya fitar a jiya. Bayan wani taro
da Jami’an tsaro na Jihar, Gwamnan ya dauki wannan mataki na dakatar da ‘Yan
Kungiyar har tsawon wani lokaci.
Kafin yau dama can Hukumar ‘Yan Sanda sun gargadi ‘Yan
Kungiyar. Bayan nan ne Gwamnati ta saka Kungiyar cikin ‘Yan tawaye, wanda
Kungiyar tace ba za ta yarda ba.
Gwamnan yace anyi hakan ne domin kawo zaman lafiya a
Jihar. Gwamnan yace zai Hukunta duk wanda ya saba wannan doka.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment