– Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantu na gaba da Sakandare za ta kawo sabon salo
– Shugaban Hukumar JAMB din yace za a saka na’urar daukar hoto a dakin jarrabawa
– JAMB din za ta kawo wani tsari domin rage matsalolin da aka fuskanta a baya
Hukumar JAMB ta canza kidan ta don kuwa tana shirin kawo
wani sabon tsari a harkar Jarrabawar Kasar. JAMB din tana shirin saka
na’urororin daukar hoto na boye a dakunan zana jarrabawa.
JAMB tace daga shekara mai zuwa, duk dakin da aka ba
damar daukar jarrabawa sai ya cika wannan sharadi. Hukumar JAMB tace sai an
saka na’urorin daukar hoto na CCTV a dakunan Jarrabawar. Shugaban JAMB din, Farfesa Ishaq
Oloyede,
ya bayyana haka a Legas.
Farfesan yace amfanin hakan shine a ga duk abin da ke
faruwa a dakin jarrabawan a ko ina a duniya. Farfesa Oloyede yace muna cikin
tafiyar canji ne, don haka dole a gani a Kasa. Farfesa yace dole kuma dakin
jarrabawa ya samu na’urar zana jarrabawa guda 250, da wasu kuma gudun ta-baci.
A baya dai Hukumar JAMB mai gudanar da jarrabawar shiga makarantu
na gaba da Sakandare a Kasar ta rage makin da ta saka a da can na samun shiga Jami’o’in
Kasar.
Muhammad Malumfashi ya rubuta wannan labari a shafin NAIJ.com Hausa
No comments:
Post a Comment