– Gwamnatin Jihar Kaduna za ta
dauki mataki kan masu tada rikici a Kudancin Jihar Kaduna
– Gwamnati tace za ta hukunta
wadanda aka samu da laifin
– Ana
ta rikici a Yankin Kudancin Jihar
Gwamnatin
Jihar Kaduna ta bayyana cewa za ta hukunta wadanda aka samu da laifin hura rikicin Yankin Kudancin
Jihar Kaduna. Wasu mutane dai sun kona Gidan wani Sarki a Yankin. Gwamnan yace
dole wadanda suka yi wannan, su dandana kudar su.
Gwamna Nasir El-Rufai yayi wannan magana ne a Fadar Sarkin Jama’a, Gwamnan ya koka da irin barnar da aka yi. Wasu matasa dai sun kona Gidan Shugaban na su. Malam El-Rufai yace wasu ‘Yan siyasa ne ke tunzura su, kuma dole a hukunta su.
Gwamnan yace za ayi bincike
game da lamarin, Sarkin Jama’a, Alhaji Isa Muhammadu ya kira Gwamnan da yayi
wani abu cikin gaggawa na mataki. Sarkin ya nemi Gwamna ya karo Jami’an tsaro a
Yankin domin kawo karshen matsalolin.
Ana ta rikici a Yankin na Kudancin Kaduna, inda Gwamnan ya taka ya je da kan sa, har wasu suka yi ta zanga-zanga. A nan wasu suka yi kokarin kai hari ga motocin da ke tawagar Gwamnan.
A biyo mu a shafin mu
na NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment