Wani
Dan Arewa ya taka rawar gani
– Wani dalibi daga Arewa ta Najeriya ya taka rawar gani a Kasar Ingila
– Marzuq Ungogo ya gama da mataki na farko a karatun digirin san a biyu
– Haziki Marzuq Ungogo ya kammala digirgir a Jami’ar Glasgow
Wani dalibi dan Arewa ya
ciri tuta a can nesa Kasar Ingila. Marzuq Ungogo ya gama da matakin farko wajen
karatun Digirin sa a Jami’ar Glasgow ta Kasar Birtaniya.
Marzuq mutumin Kasar Kano
ne, kuma yayi Digirin sa a Jami’ar nan ta Ahmadu Bello ta Zariya, inda ya
karanta Ilmin likitan dabbobi. Ko a Digirin na sa na farko dai, Marzuq ya ciri
tuta a Jami’ar, inda ya ko kammala da matakin farko watau ‘first class’ a shekarar 2014.
Wannan haziki ya samu shaidar
karantar Ilmin da ke lura da yadda magunguna ke aiki a jikin halittu watau
‘Clinical Pharmacology’ a Jami’ar Glasgow da ke Kasar Birtaniya.
Kwanaki ma dai an samu wani
gwarzo dan Arewa mai suna Adamu Tilde da ya taka rawar gani a wata Jami’ar Kasar
Hungary. Shi ma Tilde, ya kware ne a fannin ilmin dabbobi.
Allah ya kara mana irin su.
Muna matukar alfahari da wannan dalibi kuma abokin mu Marzouq. Allah ya kara masa hazaqa.
ReplyDelete