– Yau fiye da shekaru 30 ana so a ga Biredin rogo a Najeriya
– Gwamnatin Tarayya ta kashe makudan kudi a baya
Kwanakin baya aka kara tado yunkurin shirya biredi daga
rogo. Shekaru sama da 30 kenan Gwamnati na kokarin ganin an yi Biredin Rogo a
Kasar nan. Wadanda suka koyi aiki sun bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba ta
taimaka masu da kudi ba.
Lokacin Gwamnatocin baya, haka aka yi ta kai-ruwa-rana;
An koyawa mutane da dama aikin Garin rogon, sai dai duk kuwa a banza; don kuwa
Gwamantin Tarayya ba tayi aikin komai ba wajen ganin an agazawa masu wannan
harka.
Wani daga cikin wanda aka horar lokacin Shugaba Jonathan
yace tabbas sun samu koyan aiki a wancan lokaci, sai dai yanzu da kamar wuya
mutum ya samu jari daga Bankunan Manoma. Ministan Gona na lokacin Shugaba
Jonathan yayi wannan kokari, amma abin ya ci tura.
Muhammad Malumfashi ya fassara wannan a NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment