‘Riko da Sunnar Ma’aiki SAW’-Daga Bakin Imam Ustaz Sa’eed Yunus.
Assalamu Alaikum wa Rahmatul
Lah,
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah SWT wanda ya cika mana addinin mu. Babu wanda ya isa ya kara
wani abu a cikin Addini face yana da wata hujja daga Allah ko daga Manzon Allah
SAW. Ina gode masa, ina tuba gare sa, ina neman gafarar sa, ina shaidawa cewa
shi kadai yake ba shi da wani abokin tarayya. Shi ne ya shar’anta mana Addini
ya sawwaka shi, ya hukunta al’amari. Allah SWT shine wanda yayi mana ni’ima wanda
ba su kirguwa.
Ina shaida cewa Annabin Mu,
Annabi Muhammadu SAW, Bawan Allah ne kuma Manzon Sa. Shi ne wanda yayi bushara
da Al’umma, kuma Shi mutum ne tamkar sauran mutane wanda Allah SWT ya aika Shi
ya kasance rahama ga Duniya gaba daya. Allah SWT ya aiko Annabi Muhammadu SAW
domin ayi da’a gare sa kuma ayi biyayya, ba don a saba masa ba; ba don ayi kari
cikin Addini ba, ba don ayi kirkira ba. Babu Imanin da zai inganta face an yi
da’a ga Manzon Allah SAW wajen aiki. A cikin lamura, duk wanda yake so ya ci
nasara, ya bi Ma’aiki SallaLahu Alaihi Wasallam. ‘Yan uwa, ku sani cewa
nisantar abubuwa na kirkire-kirkire a rayuwa, abu ne da ke sa a ci nasara a
rayuwa. Tsira da amincin Allah su tabbata ga wannan farin jakada na Allah,
Annabi Muhammadu SAW.Mu ji tsoron Allah, mu sani cewa Allah ya aiko mana Manzo
daga cikin mu. Tsayuwa a kan abin da Annabi SAW ya zo da shi da shari’ar Manzon
Allah, cin nasara ce. Haka nisanta da kuma abin da mutane suka kirkira, wannan nasara
ce.
‘Yan uwa mu sani fa ita Bidi’a,
ita ce abin da Allah SWT bai saukar da wani dalili a kan sa ba. Lallai Manzon
mu Annabi Muhammad SAW yayi umarni da a rike Sunnah ta sa. Manzon Allah SAW
yayi wannan umarnin sau da yawa; kuma wannan umarni ya tabbata cikin Al-Kur’ani
mai girma; haka ma kuma Hadisai sun tabbatar da abin da wadannan ayoyi suka
fada game da sabawa Ma’aiki. A ji tsoron sabawa Ma’aiki, gudun musiba ta samu
mutum ko wajen mutuwa, ko a Ranar Lahira a ce da shi ba ka cikin wadanda suka
bi koyarwar Ma’aiki. Annabin Rahama SAW yana cewa a wani Hadisi da Imamu Ahmad
da Abu Dawuda da Tirmidhi da Ibn Majah suka fitar da shi daga Irbab dan Sariya
RA yake cewa: Manzon Allah SAW yace: Duk wanda ya rayu daga cikin ku, zai ga
sabani mai yawa. Saboda haka, ina kiran ku, ku rike Sunnah ta, da Sunnar
Magabata shiryayyu, ku rike ta, riko mai karfi da turaman hakora…Sannan
Annabi SAW yake cewa: Ina yi maku kashedi da abin da aka kirkira, lallai duk abin da aka
kirkire sa, fararre ne, kuma dukkan wani abu shi ake cewa Bidi’a, kuma Bidi’a bata
ce, kuma bata tana cikin wuta. Allah ka kare mu.
Abdullahi Dan Abbas RA, yana
cewa: Babu wani zamani da zai zo wa mutane, face sun kirkiro wani abu na Bidi’a,
kuma su zo su rufe Sunnar Manzon Allah. Su kife Sunnah, su kuma rayar
da Bidi’a. Dan Abbas yace wannan zai jawo masu bala’i. Abdullahi Dan Umar RAA
yana cewa: Dukkan wata Bidi’a bata ce, ko da mutane suna kallon ta mai kyau. Imam
Al-Lalaka’i ya fitar da wannan a cikin Littafin Sharh Usulul I’tiqad Ahlul-Sunnah wal Jama’a. Imamuna Malik yana
fada cewa: Babu abin da zai daidaita wannan al’ummar ta karshe, face abin da ya
gyara al’umma ta farko.
‘Yan uwa masu
girma kun ji abin da manyan Magabata, Bayin Allah suke fada game da Addini. Wani
daga cikin Magabata yana cewa: Dukkan wasu hanyoyi wadanda za a bi domin a
gane Addini, an riga an rufe su, face abin da ya dace da karantarwar Annabi
Muhammadu SAW. Imam Ibraheem Al-Nakha’iy Allah ya masa Rahama yana
cewa: Duk wanda ya kirkiri wani abu daga cikin abubuwa na Addini, wadanda ba
su cikin Addini, yana masa kallon abu ne mai kyau, kamar yana tuhumar Manzon
Allah SAW ne da cewa yayi ha’inci game da risala watau sakon Annabta. Ibraheem
Al-Nakha’iy yake cewa Allah ya fada Lallai Annabi SAW ya cika
Addini.
Allah ka azurta
mu bin hanya madaidaiciya, da koyi da Shugaban mu Annabi Muhammadu SAW. Allah
ka nisantar da mu da bin Bidi’a.
Bangare na biyu
na Huduba.
Bayan Godiya ga Allah wanda
yayi umarni da biyayya gare sa da kuma Manzon sa, Annabi SAW; wanda yayi hani
game da kirkirar Bidi’a. Ina shaidawa ba sa da Abokin Tarayya, kuma ina
shaidawa Annabi Muhammadu SAW Bawan Allah ne, Manzon Sa.
‘Yan uwa masu girma mu sani
cewa ita gaskiya ana sanin ta ne ta hanyar dalili. Ana gane gaskiya ne da
dalili na shari’a ba da yawan aikin Mutane ba. Ka da ka rudu da yawan masu
kirkirar Bidi’a; abubuwan da ba su tabbata ba cikin Addini. Allah yayi kashedi
cewa: Idan ka bi yawan mutane a ban Kasa, za su hallakar da kai. Yawa
ba shi bane abin lura, A’a, Ina dalili?
Ina mana wa’azi game da
abubuwa da suke aukuwa lokaci bayan lokaci, wasu mutane suna kirkirar abubuwa suce
Addini ne, Amma babu karantarwa a cikin Addini game da shi. Sai ka ji cewa
kawai, mun ga mutane suna yi ne kurum. Allah ya fada cewa wasu suna fadan: Mun
ga Iyayen mu ne kurum suna aikatawa…Wannan ba dalili bane, sai dai abin
da ya tabbata a Sunnah.
Mutanen da suke kokarin raya
Bidi’a, Makaryata ne kurum, suna nema su gusar da sha’awar su da yunwar da suke
ji; su dai su ci, su more. Daga nan kuma kawai sai a fara kirkirar wargi da
wasa da karya. Wadanda suke kira ga wannan al’amari suna kokarin nunawa al’umma
cewa Annabi bai isar da sako ba, suna kokarin kawo shakka ga Sunnar Manzon
Allah. ‘Yan uwa ku fadawa duk wanda yake kirkirar abin da Annabi SAW bai yi ba
cewa wannan abu yana dawo da mu baya.
‘Yan uwa masu girma, Huduba
tana fada mana cewa yaushe ne mutane za su farka daga wannan bala’i? Ina Addini
da kishi na Tauhidi? Ina riko da Kur’ani da son Manzon Allah SAW da ake takama
da shi? Lallai Annabi SAW ya fada mana cewa Musulunci ya zo bako, kuma zai koma
bako. Yau ga bakon Addini muna gani, Mutane suna ta kirkirar abin da Annabi SAW
bai yi ba. Ya ku ‘Yan uwa Musulmi, ya ku masu son Manzon Allah, ku rike Sunnar
Manzon Allah, ku kiyayi kirkirar abubuwa a cikin Addini. Ayi riko da Sunnah
kamar yadda Annabi ya koyar; za a ci nasara, kuma za a samu babban rabo. Lallai
mutane su sani cewa dukkan Bidi’a sharri ce, Lallai dukkan Bidi’a da aka danganta
ta da Addini, sharri ce. Domin ita Bidi’a tana cikin Addini ne, abin da ya
shafi mu’umala ba a kiran sa Bidi’a. Wanda ya kirkiri wani abu wanda ba ya cikin
Addini, ya kuma ce Manzon Allah SAW ne ya fada, to za a maida masa,
kamar yadda Hadisai suka nuna.
‘Yan uwa ba ku ga abin da
yake faruwa na rafkana da magagi ba ga Mutane? Wallahi daga cikin wadannan
abubuwan da suke aukuwa aka rasa gane bakin zaren, har da Bidi’ar da mutane
suka dangana ga Manzon Allah SAW.
Muna rokon Allah ka sa mu
kiyayi abin da Manzon ka ya hana mu aikatawa. Kuma Allah ka sa mu cikin wadanda
ba su alfahari. Wannan Huduba tana nunawa mutane cewa su dawo cikin hankalin
su.
Allah ka azurta mu da kyakkayawar
biyayya ga farin Jakadan ka, Annabi Muhammad SAW. Allah ka buwaiyar da Addinin
Musulunci da Musulmai ka kaskantar da Kafirci da Kafirai. Allah ka biya mana
bukatan mu…
Ameen.
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga
Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter:@Ya_waliyyi
No comments:
Post a Comment