– Daya daga cikin Ministocin Buhari ta samu babban matsayi a Majalisar Dinkin Duniya
– UN za ta nada Amina J. Mohammed a matsayin Mataimakiyar Shugaba
– Ministar tayi aiki da Shugaban Majalisar Dinkin Duniyar
Shugaba
Buhari zai rasa Minista
Da alamu Majalisar
Dinkin Duniya za ta dauke daya daga cikin Ministocin Najeriya. Amina J.
Mohammed tana dai cikin Ministocin da suka fi kowa kokari a Gwamnatin Shugaba
Buhari. Yanzu haka labarai na zuwa cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta ba ta
babban matsayi.
Jaridar Premium Times
tace an gama shirin nada Amina Mohammed a matsayin Mataimakiyar Shugabar
Majalisar Dinkin Duniya, kuma nan da wani dan lokaci za a sanar. Sai dai Fadar
Shugaban Kasa tace ba ta san wannan ba, Shugaban Kasa yace har yanzu Amina
Mohammed, Ministan Kasar ce.
Ministan tana ta kokari
wajen ganin an tsabtace muhallin Kasar. Kwanaki Gwamnati ta kaddamar da shirin
Ogoni na Neja-Delta, inda Man fetur ya gurbata.
Amina Mohammed tayi
aiki da Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, Ban-Ki Mon kafin nan. Zuwa Junairun
badi ne dai za a sake sababbin Shugabannin Majalisar ta Dinkin Duniya watau UN.
Kwanakin baya dai Shugaba Buhari ya rasa wani Ministan, har yanzu kuma ba a
maye gurbin sa ba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment