Wednesday, December 21, 2016

Shugaba Jammeh ya soki su Buhari




Shugaban Kasar Gambia yayi tir Kungiyar ECOWAS ta Afrika

 


– An nada Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda zai sasanta rikicin siyasar Kasar Gambia

 


Sai dai Yahaya Jammeh yace wannan duk ba za su sa ya janye ba

 

 Kasar Gambia: Shugaba ba zai sauka ba



Shugaban Kasar Gambia ya sanar a Gidan Talabiji cewa ba abin da zai sa ya sauka daga Shugabancin Kasar. Karshen makon can ne Shugaba Buhari da wasu Shugabannin Afrika su ka kai ziyara Kasar domin ganin Shugaba Jammeh ya amince da sakamakon zaben da ya sha kashi.
 
Shugaba Yahaya Jammeh yace dai ziyarar da su Buhari suka kai bai canza komai ba. Yace babu dalilin da zai sa ya sauka daga mulkin Kasar. Shugaban Kasar ya sanar a Talabijin cewa kawai bata lokaci ne su Buhari suke yi don kuwa yana nan daram-dam a kujerar mulki. 

Jaridar This Day ta kawo wannan labari. Shugaba Jammeh na Gambia dai yace shi ba matsoraci bane. Yace babu wanda ya isa ya karbe matsayin sa sai Allah madaukaki. Shugaba Jammeh yace su Buhari sun gama yanke hukuncin cewa sai ya ajiye mulki tun kafin su gana, yace to ba wanda ya isa.

Shugaban Kasar ta Gambia, Yahaya Jammeh dai yayi amai ya lashe; da farko ya amice da sakamakon zaben da ya fadi, daga baya kuma Shugaban Kasar yace faufau bai yarda ba. Jammeh ya fi shekara 20 yana mulki.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...