Friday, December 23, 2016

Ya kashe uban sa, ya bi uwar sa zai kashe


Wani Saurayi ya aika Uban sa lahira a Legas


Wannan Saurayi ya kuma bi uwar sa zai kashe


Yanzu haka yana can daure a Gidan Yari




Wani Saurayi mai shekaru 24 ya kashe Uban da haife sa, ya kuma yi kokarin kashe uwar sa ita ma. Wannan abu dai ya faru ne a Garin Legas. Sunan wannan yaro dai Babalola Rotimi Jr.

Alkalin Kotun Majistare da ke Ebute Meta ya nemi a tsare wannan Saurayi a Gidan Yari. Yanzu haka an yi Gidan Maza da Babalola da ke Ikoyi. Kotun ta bada umarnin a tsare Saurayin ne kamar yadda wani Jami’in tsaro na Jihar ya bada shawara.

Ana zargin Babalola Jr. da laifin kashe uban sa da kuma kokarin hallaka uwar sa da wuka. Sai dai yace shi fa ba aikata wannan laifi ba. Kotu ta bada damar belin sa a kan kudi N500, 000 tare da kawo ‘yan uwan sa na jini da za su tsaya masa. An dai daga karar yanzu haka.

Kwanaki aka gurfanar da wani matashi dan shekara 30 mai suna Tunde Ajani a gaban Kotun Majistare da ke Apapa na Garin Legas da laifin tada fitina da kuma yi wa wani Dan Sanda dukan tsiya. Hakan dai ta sa aka yankewa saurayin dauri a Gidan Yari.


[NAIJ Hausa]





No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...