...Tuni har Obama ya kira Shugaba Buhari
– Jami’an Hukumar DSS tayi wani babban kamu
– An damke daya daga cikin
manyan ‘Yan ta’addan Duniya a Najeriya
– Yanzu haka Barrack Obama ya
kira Shugaba Buhari a waya
Hukumar
DSS ta damke daya daga cikin manyan ‘Yan ta’addan Duniya a cikin Kasar nan. Har
yanzu dai ba a bayyana suna ba saboda ana cikin bincike. Wannan mutumi da aka
kama shine na uku a jerin ‘Yan ta’ddan Duniya gaba daya.
Kwanakin
nan ne kuma Hukumar ta liken asiri ta gano wani yunkuri na kai hari a Kasar
Amurka. Jaridar The Nation ce dai ta
bayyana wannan labari; tace an kama Babban Dan ta’addan Duniya a cikin Kasar
nan.
Ana
zargin wannan Dan ta’adda da kashe mutane a Duniya daga shekarar 2012 zuwa ta
2013. Yanzu haka dai Jami’an tsaro daga ko ina a Duniya sai barkowa suke yi
cikin Kasar domin su gana da wannan Dan ta’adda suyi masa tambayoyi.
Ba
a dai ba da sun aba har yanzu saboda halin bincike. Tuni dai har Shugaban Kasar
Amurka ya kira Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya domin jin yadda abin ya
faru.
No comments:
Post a Comment