Wata
yarinya mai shekara 10 a duniya ta zama uwa
– Wata Yarinya mai shekara 10 ta haihu a Kasar Kenya
– Wannan yarinya ta zama ‘yar autan uwaye a bara
– Ko shin ta ina ta samu juna biyu?
Wata karamar yarinya mai shekara
10 da haihuwa a duniya ta haifi wata itama. Wannan abin al’ajabi ya faru ne a
Kasar Kenya a shekarar bara watau 2015.
Wannan yarinya mai shekara
goma a duniya. Gladys Chelagat ta kafa tarihi, inda ta zama uwar da ta fi
kowace karanci shekaru a duniya.
Likitoci dai sun ce Gladys
ta sauka lafiya, inda ta haifi jariri mai nauyin kusan kilo uku. Sai dai da aka
yi aiki, sannan aka samu cire jaririn da aka samu. An yi wannan aiki ne a wani
Asibiti a Kasar Kenya.
Wani mutumi ne dai mai
shekara 60 yayi wa wannan karamar yarinya ciki, wannan mutumi ya kasance mai
kula da ita tun tana ‘yar karama. Wannana abu dai ya ba kowa mamaki kwarai da
gaske. Wannan abu ya faru ne a Watan Yunin bara.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment