– An kai wa Shugaban Kasa tutar
Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau
– Shugaban Kasar bai ce komai
ba game da Sabon Bidiyon Shekau
– Shekau ya soki Shugabannin Kasar
a sabon Bidiyo
Rundunar
Sojin Najeriya tace za ta cigaba da kare rayukan mutanen Kasar Arewa-maso-Gabas
da Boko Haram suka addaba a baya. An dai mikawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari
tutar Shugaban wani bangare na Boko Haram da aka samu wajen sharer Dajin
Sambisa inda aka fatattaki ‘Yan ta’addan.
Manjo
Janar Lucky Irabor ne ya mikawa Shugaban Kasar kuma Kwamandon Sojin Kasar gaba
daya tutar Boko Haram din. Sai dai Shugaban Kasar bai ce komai ba game da wani
sabon Bidiyo na Abubakar Shekau din inda yake karyata maganar Sojin Najeriya na
cewa an fatattake ‘Yan Boko Haram.
Jaridar
The Cable ta rahoto cewa da safiyar Jumu’a aka mikawa Shugaban Kasar tutar Boko
Haram din da suka saba kafawa a matsayin sun kafa Daula. Shugaban Kasar ya
jinjinawa Sojojin Najeriyar da kwazon su.
Shekau
ya fitar da wannan Bidiyo mai tsawon fiye da Minti 10, inda ya caccaki su Janar
Buratai da Kasashen da ke ba Kasar taimako, yace su Allah ne zai taimake su.
Tuni da Sojin Kasar ta bayyana Bidiyon a matsayin Farfagandar banza.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment