Tuesday, December 27, 2016

Dan shekara 11 ya kama Shugaban Kasa da sata


– Wani karamin yaro dan shekara 11 ya kai karar Shugaban Kasa Kotu


– Yaron na karar Shugaban Kasar da wanke kalaman sa, ya shanye


– Kotu ta dakatar da karar har zuwa wani lokaci



Wani karamin yaro ya kai Shugaban Kasar Pakistan Kotu inda yake karar Shugaba Mamnoon Hussein da satar jawabin sa. Wannan yaro ya bayyana cewa shi ya rubuta jawabin da Shugaban Kasar ya kama ya wanke, ya shanye, ya zuba tamkar nasa.

Wannan yaro mai suna Muhammad Sabeel Haider yace shi ya rubuta jawaban da Shugaba Mamnoon na Kasar yayi aman su. Yanzu haka dai wannan yaro ya maka Shugaban Kasar kara a Babban Kotun Islamabad.

Mahaifin Yaron, Naseem Abbas Nasir ne ya shigar da wannan kara a madadin dan sa mai shekara 11 da haihuwa. Yaron yace shi ya rubuta jawabin domin tunawa da MA Jinnah wanda ya kirkiri Kasar Pakistan.

Yaron yace wani ne ya saci takardar ba tare da ya sani ba. Kamar yadda Jaridar Express Tribune ta rahoto, yanzu haka Alkali Aamer Farouk ya dakatar da wannan kara tukuna. Haidar yace an fada masa cewa za ayi amfani da jawabin nasa, amma cewa aka yi wata Yarinya ce za tayi ba Shugaban Kasa ba.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...