Monday, December 12, 2016

Duk wanda ya shiga tsarin MMM ya aikata haramun Inji Fasto

– Fasto Sulaiman Johnson yace tsarin MMM bai halarta ba 

 


– Limamin Cocin Omega Fire International yayi tir da tsarin MMM

 


– Yace masu shiga wannan tsari suna bukatar addu’a



 Mutumin da ya kirkiro MMM yace ba zai rushe ba

  
Babban Faston Cocin Omega Fire Ministry International yayi kaca-kaca da tsarin nan na cacar MMM. Babban Faston ya kira mabiyan sa da su guji shiga irin wannan tsari. Mutane da dama dai sun shiga cikin wannan tsari na MMM tsindum. 
 
Idan har mutum ya saka kudin sa, za a ribanya masa, sai dai Fasto Sulaiman yace hakan bai hallata ba. Babban Limamin yace duk irin wannan tsari ba su da kyau a addini, yace kuma aikin shaidan ne.

Fasto Sulaiman yace ana tatsar wasu ne domin wasu su amfana; ya kira wanna tsari da na Shaidan, ya kuma ce duk wadanda suke ciki shaidanu ne. Faston dai yace wani Dan Damfara ne ya kirkiro wannan tsarin, kuma Mutumim Amurka, yace Kiristan kirki bai kamata ya shiga wannan haka ba. 

Sai dai kamar daga Kasar Russia aka kawo wanna tsari. Shi dai Faston ya kira mutanen sa, da su nemo aikin kwarai su tuba. Yace wadanda suka shiga wannan cacar suna bukatar addu’ar gaske.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...