‘Riko da Sunnah II-Daga Bakin Imam Ustaz Dr. Sa’eed Yunus
Assalamu Alaikum wa Rahmatul
Lah,
Dukkan yabo da godiya sun
tabbata ga Allah SWT wanda ya aiko Manzon Sa da shiriya da Addini na gaskiya da
ya rinjaye sauran Addinai. Ina gode masa, ina jinjina masa, ina tuba gare sa,
ina neman gafarar sa, ina shaidawa cewa shi kadai yake ba shi da wani abokin
tarayya. Ya tsarkaka da duk abin da Azzalumai suke fada. Shaidar da za tayi
amfani Ranar da ‘Ya ‘ya da dukiya ba su da amfani.
Ina shaidawa cewa Annabi
Muhammadu, bawa ne kuma Manzom Allah. Allah ya aiko sa domin yayi bushara da
kuma gargadi. Annabi SAW lallai ya isar da sako. Allah kuma ya daga darajar sa
da matsayin sa. Sannan kuma Allah ya gusar da kuskure gare sa. Allah ya saka
kaskanci da wulakanci ga wadanda suka sabawa Manzon sa. Lallai mu Masoya Manzon
Allah SAW ne, kuma muna rokon Allah ya tabbatar da mu a kan haka. Allah ka dada
tsira ga Farin Jakada; Annabi Muhammadu SAW da Sahaban sa da iyalan sa da
sauran wadanda suka bi tafarkin sa zuwa Ranar karshe.
Bayan Haka:
Yayin da fitina suka watsu a
Doran Kasa cikin Al’umma, ana ta Hudubobi, gaskiya ta hadu da karya. Ana cikin
rudu Jama’a! Mafita day ace; A ji tsoron Allah. Tsoron Allah kadai zai haska
hanya. Duk wanda Allah ya azurta da tsoron sa, ya samu gam-da-ka-tar.
Daga cikin masu batar da
mutane, za ka ji su da zakin baki. Allah dai yace idan har ku ka ji tsoron sa,
zai gafarta maku zunuban ku, ya kuma azurta ku arziki mai yawa. Ubangiji kuma
yace Idan kun ji tsoron sa, zai ba ku mafita, domin Allah mai falala ne. ‘Yan
uwa tsoron Allah babbar kyauta ce, duk wanda Allah ya azurta da tsoron sa, ya
sami kubuta daga hanyar Shaidn. Allah ne yace idan ku ka yi Imani ku ka ji
tsoro na, Allah zai ribanye masu haske ya kuma gafarta masu, domin Shi mai Gafara
ne kuma mai Rahama.
Imam Yahaya dan Yahaya yake
cewa tsayuwa tsayin daka ya fi tafiya Jihadi. Abu Ubayda Dan Salma kuwa yake
cewa wadanda suka rike Sunnah tamkar sun rike garwashi ne. Yanzu kuwa kana iya
cewa tamkar a doke ka da takobi; dubi yadda ake wulakanci a yau, Musulmai suna
cikin kaskanci; sun kawo abubuwan da ba su cikin karantarwar Addinin Manzon Allah;
sun hada gaskiya da karua, Sunnah ta zama bidi’a. Yaushe ne za mu fita daga
wannan rudu? Yaushe ne za mu banbamce tsakanin Makiyi na fili da Masoyi domin
Allah.
‘Yanuwa ta ya za
muyi hidima ga Addinin Allah? Ta ya za mu kare Sunnar Ma’aiki? ‘Yan uwa masu
rubutu a Jaridu, ta ya za ku yi tallar Addinin mu, kuma a san cewa abin da ba
karantarwar SAW ba, ya sabawa Addinin mu. Ta ya za kuyi wa mutane bayani har ya
zama ba za a samu ragonta ba ko wuce gona da iri? Ina makarantun Islamiyyun mu?
Ina makarantun Hardar Al-Qur’ani? Ya ku dalibai na Sunnah, idan har da gaske ku
ke, mu ga Sunnah a Kasa. Ya kai wanda kake Musulmi, ka nunawa wanda ba Musulmi
ba cewa lallai Addinin Musulunci addini ne na gaskiya. ‘Yanuwa masu girma ku
sani cewa idan kun yi haka, Allah zai cika maku alkawarin da yayi maku. Gare Sa
ne ake samun nasara da kuma dacewa, Allah ka bami nasara ka sa mu dace.
Huduba ta biyu, bayan godiya
ga Allah; wanda ya rarrabe tsakanin hanya ta gaskiya da ta karya, wanda ya aiko
Manzani na sa masu yawa masu gargadi don ka da wasu su ce a Ranar Lahira Allah
bai aiko da Manzo ba. Ina shaidawa Allah shi kadai yake ba shi da abokin tarayya,
ina shaidawa cewa Annabi Muhammadu SAW Bawan Allah ne kuma Manzon sa ne.
Hakanan Sahaban sa da Iyalan sa, tsira da amincin Allah ya kara tabbata a gare
su.
Bayan Haka:
‘Yan uwa mu ji tsoron Allah,
mu rike Sunnar Manzon Allah SAW, mu sani cewa lallai Allah ya zabe mu ne, don
haka ne ya saka mu cikin al’ummar sa. Kuma mu sani cewa mafi alherin haske shi
ne Al-Kur’ani, kuma Mafificiyar shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammad SAW
kuma mafi sharrin al’amari shine wanda aka kirkira aka danganta shi da Annabi
Muhammad SAW, sannan kuma duk abin da aka kirkira a Addini Bidi’a ne, kuma duk
Bidi’a bata ce.
‘Yanuwa masu girma, daga
cikin Rahamar Allah ga abayin sa, Allah ya saukar da littafi na Al-Kur’ani; wanda
ya kasance haske ne a kowane zamani, kuma Allah ya azurta wasu mutane masu
tsayuwar daka suna karantar da Jama’a da kokarin ganin mutane a kan tafarkin
Manzon Allah. ‘Yan uwa ka da ku manta idan kiyama ta tashi, Allah zai kira wasu
Mala’iku yace masu: Ga wasu bayi na sun canza bayan tafiyar Manzon Allah SAW.
Annabi yana kokarin kiran su, sai a fada masa cewa ai sun canza, sun canza…Allah
ka da ka sa mu cikin wadannan mutane. ‘Yan uwa masu girma, mu sani cewa hakki
ne a kawunan mu gaba daya duk wani Musulmi da yake rayuwa a doron Kasa,
gwargwadon abin da zai iya, ya san cewa wajibi ne a kan sa ya raya Sunnar
Manzon Allah SAW, ya taimaki Musulmai, ya karantar da su abin da ya sani; hakan
ne hanyar shiga Aljanna. ‘Yan uwa muna da wata hanya ta shiga Addini ne ba ta
Annabi Muhammad Al-Mustafa ba? Ba mu da hanyar da ta wuce ta sa da ta Sahabbai
wanda sune shiryayyun wannan al’umma. Ya kai me neman kubuta, ina kiran ka da
riko da Sunnah, ka yi biyayya da karantarwar Manzon Allah da ta Sahabbai. Ina
gargadin ka da ruduwa da wasu mutane da suke fitar da mutane da harshen su; da
Hadisan suna karya, da karatun san a Kur’ani. Za su kasance masu zakin baki,
amma suna adawa ne da Al-Kur’ani, ka sani cewa gaskiya ba ta bukatar ado.
Gaskiya kuma ba ta bukatar yawa, sai dai hujja da dalili. Allah yana fada mana
cewa idan ka bi yawan mutane za su batar da kai daga hanyar Allah.
‘Yan uwa a yau muna fama da
kalubale a matsayin mu na Musulmai masu nema mu raya Sunnar Ma’aiki SAW, saboda
wasu sun shigar da wasu abubuwa cikin Sunnar Ma’aiki. Wadannan mutane suna
neman daukaka, suna nema a san su a Duniya. Daraja fa a hannun Allah take.
Allah ne ya fitar da Annabi Musa AS daga Gidan kaskanci zuwa Gidan Fir’auna.
Allah ne ya raya sa har ya zama abin da zai zama a Gidan Fir’auna. Allah ne ya
fitar da Manzon sa SAW a Maraya. Allah ne kuma ya fitar da Annabin sa Yusufu AS
daga kasakanci. Ya kai mai tsoron Allah, ina kiran ka, ka yarda Allah ne ke ba
da daraja ba yawan mutane ba. Ka tuna cewa wata rana za ka wayi gari kai daya a
kabari.
‘Yan uwa mu yi kokari mu
cike duk wata gaba a karantar da mutane Sunnah cikin kwanciyar hankali; babu
zagi, ko zolaya ko habaici. ‘Yan uwa mu nunawa Allah cewa mu mutanen kirki ne,
domin wallahi idan har muka nunawa mutane cewa haka, Alhali ba hakan bane, mun
shiga wani hali.
Lallai Kasar mu tana bukatar
Addu’a, akwai bukatar a karantar da mutane Sunnah. Rashin sanin Sunnah ce ta sa
mutane suke tafiya a baude. Dama Manzon Allah SAW yace idan karshen zamani ya
zo, mutane za su kasance cikin rudu sai wanda suka yi riko da Sunnah. Babban al’amari
shine tsoron Allah.
Sannan Huduba tana cewa muyi
Salati ga Annabi Muhammad SAW. Addu’a.
Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga
Masallacin I.T.N-Zaria.
Twitter:@Ya_waliyyi
Sorry for being late...
ReplyDelete