Saturday, December 31, 2016

HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA

HUDUBAR JUMA’A DAGA MIMBARIN ITN-ZARIA




'Dagewa wajen neman abin dogaro da kai'-Daga Bakin Imam Dr. Mustapha Isa Qasim


A’udhu BilLahi minasshaidan Ar-Rajim,
BismilLahir Rahman Ar-Raheem,
‘Yan uwa Musulmi, Assalamu Alaikum wa Rahmatul Lah wa Barakatuh,
Muna masu godiya ga Allah Madaukakin Sarki godiya da ya kawo mu wannan Rana ta Jumu’a. Allah ya sa mu dace da sa’ar da ake gafarta zunubi a wannan Rana. Amin.
Wannan Huduba tamu tana magana ne a game da neman halaliya watau abin dogaro da kai. Yana da muhimmaci a jawo hankalin ‘Yan uwa a game da wannan batu, domin kuwa shine asasi na rayuwa. Musulunci ya kafa rayuwa a kan neman abin dogoro; aiki, noma, kasuwanci domin kuwa akwai albarka a ciki. Ta haka ne Mutum zai kasance ya samu abin da zai ci tare da Iyalin Sa na Halal.
Muna godiya ga Allah Madaukakin Sarki, muna neman taimakon Sa, Muna neman tsari daga munanan ayyukan mu. Duk wanda Allah SWT ya shiryar shi ne shiryayye, wanda kuma Ya batar, babu wanda zai shiryar da shi. Muna neman shiriya daga Allah SWT shi kadai. Muna kuma shaidawa Allah shi kadai yake, babu wani abin bauta da gaskiya face Shi. Sannan Muna yin shaida cewa Annabin Mu, Annabi Muhammadu SAW, Bawan Allah ne kuma Manzon Sa wanda Allah SWT ya aiko sa da Addini na Gaskiya.
‘Yan uwa wajibi ne mu ji tsoron wajen neman Halal. Musulunci dai Imani ne na gaskiya, sai dai Mutum ba ya zama da Imani ba tare da aiki ba. A duk lokacin da Allah Madaukakin Sarki ya ambaci cewa ayi Imani, sai an ambaci cewa ayi aiki na gari. Yana daga cikin aiki na gari; neman arziki na halal. Ba a nufin cewa Mutum zai samu aiki mai kyau kawai yayin da Mutum ya je Masallaci ko Aikin Hajji, A’a, Har Mutumin da yake noma, idan har yayi da niyya kyakkyawa tare da bin shari’a, wannan ya zama Ibada. Watau dai Dan kasuwa, Ibada yake yi, Haka Dan Makaranta… Allah ya ambaci Imani da aiki na gari a wurare masu dinbin yawa a cikin Al-Kur’ani.
‘Yan uwa bai halatta ga Musulmi ya zama mai kasala wajen neman arzikin sa ba. Ka da Mutum yace shi ba zai yi wani aiki; kasuwa ko noma dsr ba domin shi ya kebantu da ibada. Kuskure ne haka, ko Mutum yace shi ya dogara da Allah mai girma domin Shi yake badawa. Aya cikin Suratul Jumu’a tana da umarni a fita a nemi arziki cikin Kasa. Haka bai hallata Mutum ya dogara da Sadaka ko kyauta wajen wani ba. Abin da ya dace shine idan Mutum ya cancanci Zakka ko wata Sadaka, sai ya karba, ba ya zama yana jira a kawo masa ba. Bai hallata mutum mai karfi da lafiya ya rika jira a kawo masu sadaka ko wani taimako ba, wannan ba tawakalli bane illa kuskure. Matukar Mutum ya fita neman arziki na Allah, to Ubangiji zai ba sa. Kamar yadda Manzo SAW yake cewa bai halatta a ba Mutum, mai karfi-mikakke Sadaka ba. Sannan kuma idan har Mutum ya rayu a haka zai zama cikin wulakanci da kaskanci har ma suna fada cewa: Allah ya ba ku, mu samu…ka da Mutum ya zama kullum shi ne mai karba, domin kuwa hannun da ke mikawa ya fi alheri a kan hannun da ke karba. Ina laifin ko da kana karba, wata rana ka zama mai badawa? Haka dai kuma akwai wani Hadisi daga Manzon Allah SAW wanda yake cewa: Roko da bara da neman taimako, Mutane ba za su daina wannan ba, har sai sun hadu da Allah SWT a Ranar Lahira, babu wani yanki na tsoka a jikin fuskan su. Naman su duk zai sale, daga an hange su, za a gane cewa sun zama masu bara hannun Mutane a Duniya.
A game da dogaro da kai; Manzon Allah SAW yana cewa: Daya daga cikin ku, ya dauki gatari da igiya ya saro itace a daji, ya dauko a bayan sa, ya saida, ya fi masa alheri a kan ya tambayi Mutane, watakila su ba sa, ko kuma su hana sa. Idan har Mutum ya lura da wannan, yana nuna cewa ya kamata Musulmi mai karfi ya fita ya nema na sa, Idan har Mutum ya fita, lallai kuwa Allah SWT zai ba sa. Allah SWT kuwa yana cewa: Ku nemi arziki a wajen Allah domin shi kadai yake badawa. Duk wanda ka gani da Arziki, to Allah SWT ne ya ba sa, don kuwa ba shi Mutum ne ya ba kan sa ba, kai ma idan ka nema sai ya ba ka. Sai dai kuma ba a nufin cewa Ubangiji zai ba kowa daidai wadaida, wannan rabo ne na Allah mai Girma. Don haka ka da ka ji haushin wani don ya fi ka, Allah SWT zai ba ka gwargwadon abin da kake bukata. Duk wanda aka dai ba, ya zama jarrabawa gare sa; haka wanda bai samu ba, hakuri zai zama jarrabawa gare sa.
Mu sani cewa daga cikin neman abin dogaro da kai akwai abubuwa da dama; kiwo, sana’a, kasuwanci, noma, aiki irin na Gwamnati. Idan muka duba Aikin Gwamnati yayi wahala kwarai, amma noma kam Ubangiji yana saukar da ruwa ba tare da bambance gonar wane da wane ba. Kowa dai na iya yin aikin gona, ko kuwa Mutum ya shiga kasuwanci dsr. Idan har muka fahimci cewa babu wanda zai yi mana shikenan, haka neman Dukiya ta ke. Mu sani cewa kasuwanci har Allah SWT ya hada sa da Ibadar Allah. Manzon SAW kuwa yana cewa: Dan Kasuwa Mai gaskiya-Amintacce, yana tare da Shahidai a Ranar Kiyama.
To ‘Yan uwa Musulmi, wannan kenan. Amma abin da za ayi magana a kai da karfafawa shine noma. Dole mu fuskanci wannan harka ta noma musamman a irin wannan lokaci; Muna fama da matsalar tattalin arziki, ga kuma Jama’a, ga filin noma ga kuma ruwan sama. Sai dai ya zama babu wannan zuciyar a yanzu, duk da cewa Iyayen mu da noma suka taso. Kai bari ma, ba nan kadai ba, kaf Kasar nan, an ci da ita da arzikin noman auduga da gyada dsr, mun san wannan. Yanzu an bar wannan an komawa wani abu dabam duk da Allah SWT yana nuna mana albarkar noma. Babu wani haraji da ake biya na ruwan sama domin noma, ya rage ka tona Kasa, ka shuka, sai a samu tsiro da izinin Allah. Allah SWT ne yake cewa ya mana tanadi tare da gonakin mu a cikin Al-Kur’ani.
‘Yan uwa Musulmi, muyi tunani da irin abubuwan da ke faruwa a Kasar nan. Ka da mu zama ci ma zaune; mu zama sai dai a sayo kaya daga Kasashen waje domin mu ci. Yaushe Mutum zai kashe dan albashin sa wajen sayan shinkafa? Da ace Mutum zai noma ta, da zai sami abin da zai ci tare da Iyalin sa, har ya ba wasu, yana mai fitar da Zakka don Allah SWT yace Arziki ne ga Bayin Sa.
Ya kamata Gwamnonin mu na Arewa suyi tunani, su duba su ga abin da ya faru tsakanin Jihar Kebbi da Jihar Legas. Yanzu haka ana sayar da buhun shinkafa ta Kebbi kan kudi N12, 000 a Jihar Legas. Meyasa sauran Jihohin mu ba za su yi haka ba? Me zai hana Sokoto da Zamfara su hada kai? Me zai hana Jihohin Kano da Katsina, ko Kaduna da Neja, ko Yobe da Borno, da su Bauchi da Gombe? Idan har aka yi haka mun daina maganar shigo da abinci daga Kasar waje. Ya kamata mu lura da wannan, ka da mu zama ci-ma zaune. Koa bin kunya ka ga ana sayar da hatsin da muka noma ga masu giya. Daga karshe aje ayi giya, Direbobi su sha, ayi ta kashe Mutane a hanya.
Wannan dai matashiya ce, kuma lallai ba mu makara ba. Muna sa ran cewa zuwa shekara mai zuwa za a samu karin yawan masu noma da amfanin gona ba tare da mun dogara daga Kasashen waje ba.
Allah ka shiryar da mu da Shugabannin mu, ya sa mu cika da Imani.
Ameen.



Muhammad Malumfashi yayi aikin wannan huduba daga Masallacin I.T.N-Zaria.
Muhammadmalumfashi@gmail.com          
Twitter: @Ya_waliyyi


An mikawa Shugaba Buhari tutar Shekau


– An kai wa Shugaban Kasa tutar Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau


– Shugaban Kasar bai ce komai ba game da Sabon Bidiyon Shekau


– Shekau ya soki Shugabannin Kasar a sabon Bidiyo




Rundunar Sojin Najeriya tace za ta cigaba da kare rayukan mutanen Kasar Arewa-maso-Gabas da Boko Haram suka addaba a baya. An dai mikawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tutar Shugaban wani bangare na Boko Haram da aka samu wajen sharer Dajin Sambisa inda aka fatattaki ‘Yan ta’addan.

Manjo Janar Lucky Irabor ne ya mikawa Shugaban Kasar kuma Kwamandon Sojin Kasar gaba daya tutar Boko Haram din. Sai dai Shugaban Kasar bai ce komai ba game da wani sabon Bidiyo na Abubakar Shekau din inda yake karyata maganar Sojin Najeriya na cewa an fatattake ‘Yan Boko Haram.


Jaridar The Cable ta rahoto cewa da safiyar Jumu’a aka mikawa Shugaban Kasar tutar Boko Haram din da suka saba kafawa a matsayin sun kafa Daula. Shugaban Kasar ya jinjinawa Sojojin Najeriyar da kwazon su.

Shekau ya fitar da wannan Bidiyo mai tsawon fiye da Minti 10, inda ya caccaki su Janar Buratai da Kasashen da ke ba Kasar taimako, yace su Allah ne zai taimake su. Tuni da Sojin Kasar ta bayyana Bidiyon a matsayin Farfagandar banza.



[NAIJ Hausa]


Babu maganar sulhu da Dogara-Honarabul Jibrin


Dan Majalisan da aka kora ‘Jibrin’ ya karyata rade-raden sulhu



– Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Tarayya, Abdul Jibrin ya bayyana cewa har yanzu yana kan bakan sa


Jiya an rahoto cewa ya shirya zama domin ayi sulhu da Shugaba Yakubu Dogara


– Hon. Jibrin yace wannan karyar banza ce, asali ma yanzu ya fara




A jiya da rana ne Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Hon. Abdulmumuni Jibrin wanda ke wakiltar mazabar Kiru/Bebeji na Jihar Kano ya shirya yin sulhu da Shugaban Majalisar, Yakubu Dogara.

A jerin wasu sakonni da Dan Majalisar ya aika ta shafin Twitter, ya bayyana cewa wasu daga cikn yaran Shugaban Majalisar, Yakubu Dogara ne da wannan danyen aiki. Jibrin yace Turaki Hassan ne ya yada wannan rade-radin na karya.  Yace yana nan kan bakan sa, babu gudu-ba ja da baya.

Honarabul Jibrin yace babu wani sasantawa da yake kokarin yi da Kakakin Majalisar; Yakubu Dogara ko ta wasu ‘Yan Majalisar ko Dattawan Kasar kamar yadda ake rade-radi. Yace nan gaba kadan ma zai tona wasu asirin.

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta tsige Tsohon Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar, Abdulmumuni Jibrin bayan da ya zargi Shugaban Majalisar wakilan Kasar, Dogara Yakubu da wasun su da laifin handame wasu kudi daga kasafin bana.





[NAIJ Hausa]

Friday, December 30, 2016

NAFDAC tayi gargadi game da shinkafar roba


Hukumar NAFDAC ta gargade ‘Yan Najeriya da cin shinkafar nan ta roba


Shinkafar ba ta da Rajistar NAFDAC


Wannan Shinkafa dai na da illa ga lafiyar mutum




Hukumar kula da Abinci da Magunguna a Kasar nan watau NAFDAC ta gargadi Jama’a da su bi a hankali da Shinkafar nan da ake cewa ta roba. Hukumar tace asalin Shinkafar ba wai ta roba ba ce, sai dai gurbataciyya.

Hukumar ta ce har wa yau, wannan Shinkafa ba ta da ragistar NAFDAC da sauran bayanai da ke nuna daga inda Shinkafar ta fito. Shugaban Hukamar NAFDAC din mai kula da magunguna da Abinci, Yetunde Oni tace bai dace a rika cin irin wannan Shinkafa ko wanin sa ba.

NAFDAC din ta bayyana cewa za a kona irin wadannan Shinkafa da Hukumar kwastam ta Najeriya ta karbe. A wani Bincike da Hukumar tayi a Dakin taro, an gano matsaloli tattare da kwayar shinkafar.

Yayin da Kirismetin nan ya zo kuma, Mutane da dama sun shiga neman shinkafar gida a Najeriya. Wurare irin su Cross-River abin ba a cewa komai don kuwa kowa na neman shinkafar biki mai dan araha. Hukumar Dillacin Labarai ta dauko wannan rahoto daga Calabar. Wani daga cikin mazauna yankin yace shinkafar gida ta fi araha, kuma ga dadi.




[NAIJ Hausa]

Shekau ya gargadi Buhari a sabon Bidiyo


– Abubakar Shekau ya kara nanata cewa tsarin Damukaradiyya kafirci ne


– Shekau ya soki Shugabannin Sojin Najeriya


– Shugaban Boko Haram ya kira Buhari ya tuba kafin ya komawa Ubangiji





Kamar dai yadda muka fada, a jiya ne aka sanu wani sabon Bidiyo na Abubakar Shekau na Boko Haram inda yake karyata maganar Sojin Najeriya na cewa an fatattake ‘Yan Boko Haram. Shekau ya fitar da wannan Bidiyo mai tsawon fiye da Minti 10.

Abubakar Shekau ya soki Damukaradiyya a matsayin tsarin Kafirci yace shi Doka da hukuncin Allah kadai ya sani. Shekau din ya kuma soki Shugaba Buhari da sauran Musulmai da suka yi murnar Bikin Kirismeti, yace wannan ya sabawa koyarwar Addini. Sannan yace babu abin da ya hada Kirista da Nana Maryamu.



Abubakar Shekau ya nemi Buhari ya tuba a matsayin sa na tsoho wanda ya wuce shekaru 70, watau ya bar wannan tsari na Damukaradiyya da Kafirci. Shekau ya kira Shugabannin Kasar da aladu da birai a cikin wani sakon dabam na larabci.

Shugaban wani bangare na Boko Haram din, ya kira mai magana da bakin Sojin Kasar nan, Kukasheka da karamin alhaki. Ya kuma caccaki su Janar Buratai da Kasashen da ke ba su taimako, yace su Allah ne zai taimake su. Tuni da Sojin Kasar ta bayyana Bidiyon a matsayin Farfagandar banza.




[NAIJ Hausa]

Abubuwa 10 da Shekau ya fada cikin sabon bidiyo



– Yayin da Sambisa ta fadi daga hannun ‘Yan Boko Haram sai ga Abubakar Shekau ya bayyana


– Abubakar Shekau yace Rundunar Sojin Najeriya karya take yi


– Shekau yace ba dai mutum ba sai Ubangiji






A jiya ne aka sanu wani sabon Bidiyo na Abubakar Shekau na Boko Haram inda yake karyata maganar Sojin Najeriya na cewa an fatattake su watau Boko Haram daga Sambisa. Shekau ya bayyana abubuwa da dama a sakon na sa, kamar haka:

1.      Karyar banza ce ace an fatattaki ‘Yan Boko Haram.
2.      Ubangiji ne kadai ke da iko a kan su ba Sojin Najeriya ba.
3.      Shekau yace karfi ba a bakin Bindiga ta ke ba, sai dai mai Duka.
4.      Maganar cewa an kama ‘Yan Boko Haram har fiye da 1200 karyar banza ce.
5.      Shekau ya gargadi Kasashen Duniya irin su Jamus, Faransa, Italiya da sauran su.
6.      Shekau ya kara sukar tsarin Damukaradiyya da kafirci.
7.      Abubakar Shekau yace ba su san komai ba sai Littafin Kur’ani.
8.      A kan wani dalili Shugaba Buhari da sauran Musulmai za su rika Bikin Kiresmeti wanda ba koyarwar Yesu ba ne?
9.      Imani ke kara taimakon su ba kayan yaki ba.
10.  Ran san a hannun Allah Madaukaki ba wani ba.

Dama can Sojin Kasar tace an samu Littafi mai tsarki-Al Kur’ani wanda Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau yake amfani da shi a Dajin Sambisa. Sojin Kasar dai a Ranar Alhamis sun rusa kwaryar ‘Yan ta’addan na Boko Haram da ke cikin Dajin Sambisa.


[Daga NAIJ Hausa]


Thursday, December 29, 2016

Babban Ma’aikacin Gwamnati yayi gaba da motoci 40


Ka ji sirrin Gwamnatin Buhari na Yakar sata a Kasa




– Gwamnatin Shugaba Buhari na bi a hankali wajen yaki da rashawa a Kasar


– Ministan watsa labarai na Kasar ya bayyana haka


– Alhaji Lai Muhammad yace wasu suna kokarin nuna ba haka lamarin yake ba




Ministan watsa labarai da al’adu na Kasar nan, Alhaji Lai Muhammad, ya bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Buhari na bi a hankali wajen fada da cin hanci da rashawa a Najeriya. Ministan ne dai ya bayyana haka da kan sa a Yau da yake Legas.

Hakan na zuwa ne bayan da Lai Muhammad din yace an kama wani Babban Jami’in Gwamnati da yayi awon gaba da manyan motoci kirar SUV har guda 40. Wani Sakataren din-din-din ya kasa-ya rabawa kan sa wadannan motoci shi kadai ba tare da ko Bismillah ba.

Lai Muhammad ya bayyana irin matakan da Gwamnatin Kasar ta ke bi domin hana cin hanci da rashawa. Lai Muhammad yace an kawo tsarin nan na asusun bai daya watau TSA, sannan kuma an nada Kwamiti da dama domin su tattara abin da Gwamnati ta karbo daga hannun barayin Kasar.

Kwanan nan ne ma dai Gwamnatin ta kawo wani tsari na tona asiri-ka-samu-kason ka. Sannan kuma an gano ma’aikatan bogi da dama wanda albashin sun a shekara ya kai Naira Biliyan 200.


[NAIJ Hausa]


Ka ji labarin Faston da ke kai Musulmai aikin Hajji?


– An samu labarin wani Fasto da kan kai Musulmai zuwa Kasa mai tsarki domin aikin Hajji


– Fasto ayodele dai ya saba taimakawa gajiyayyu da marasa karfi


– Faston shi ne Babban Limamin Cocin INRI da ke Garin Legas





Ko ka taba jin labarin wani Fasto da kan kai Musulmai zuwa Kasa mai tsarki domin sauke faralli? NAIJ.com ta zagaya, ta gano guda, har ta tattauna da shi domin jin ya abin yake. Wannan ba kowa bane sai Fasto Elijiah Babatunde Ayodele.

Fasto Ayodele wanda shine Babban Limamin cocin INRI Spiritual Evangelical da ke Garin Legas yace ba aikin da yake sha’awa irin kula da marayu da zaurawa marasa hali a cikin al’umma. Yace burin sa ya kowa cikin farin ciki.

Kwanan nan ne ma Faston ya raba sama da buhuna 4,000 ga marasa hali saboda Bukukuwan Kirismeti. Faston yana da Gidauniya wanda ke daukar nauyin har matan Musulmai zuwa Kasar Saudiyya domin su sauke farali. Faston ya kan yi haka kuma ga Takwarorin su Musulmai.

A wata Duniyar kuma, An samu Littafi mai tsarki-Al Kur’ani wanda Shugaban Kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau yake amfani da shi a wajen sharer Dajin Sambisa. Sojin Kasar dai a Ranar Alhamis dinnan sun rusa kwaryar ‘Yan ta’addan na Boko Haram da ke cikin Dajin Sambisa.



[NAIJ Hausa]




An koma cin naman kare a Ekiti


Jama’a sun komawa naman kare a Jihar Ekiti


Duk inda ka je kurum da naman kare ake dagargajewa


Ana sayar da karnuka 'yan wata uku N500




Yanzu haka Karnuka sun fara bacewa a Jihar Ekiti, domin kuwa duk inda ka shiga cin abinci sai dai ka ga naman kare a cikin miya. Mutanen Jihar Ekiti dai sun komawa naman karnuka. Hukumar Dillacin labarai na Kasa ta bada wannan labari.

A Garuruwa irin su Ise-Ekiti, Ado-Ekiti, Ikere-Ekiti da sauran su naman Karen ya zama wani kayan Gabas, ko ina rububin kare ake yi. A gidaje da wuraren cin abinci ma da Gidan ruwa, ko ina kare kurum ake babbakawa ba kama hannun yaro.

Yanzu haka har farfesun kare ake yi a wasu wuraren.  Abin dai har ta kai babu karnuka a kan titi, don kuwa tuni sun shige tukunya. A na sayar da jariran karnuka a kan N500, manya kuma su kan kai har N15000; ain dai, iya kudin ka, iya shagalin ka.

A watan Agusta Gwamna Fayose na Jihar ya sa hannu kan wata doka da ta haramta kiwon shanu da sauran dabbobin noma a Jihar, Dokar tace duk wanda aka kama ya saba doka, za a daure sa na rabin shekaru kuma babu damar karbar tara. Dokar ta haramta kiwo daga karfe 6 na yamma har zuwa 7 na safe. Sai dai masana sun ce naman kare yana da illa kwarai a jikin Dan Adam.


 [NAIJ Hausa]



Ashe Makafi na satar amsar Jarrabawa



Jami’ar WAEC ya bayyana cewa ashe mafi yawanci makafi satar amsa suke yi lokacin jarrabawa


Misis Francis Iweha-Onukwu tace rashin kintsi ke jawo haka


An kira Gwamnati ta kara karfi wajen harkar ilmi



Wata Jami’ar Jarrabawar WAEC ta Yammacin Afrika, ta bayyana cewa ashe mafi yawanci makafi masu rubuta jarrabwar, satar amsa suke yi domin su samu nasara. Jami’ar tace hakan na bayuwa ne saboda rashin shiryawa Jarrabawar da kyau.

An dai kira Gwamnatin Kasar ta kara karfi wajen harkar ilmi gaba daya. Hukumar Jarrabawar tace mafi yawanci, Makafi kan hada kai da ‘Yan uwan su ne suyi satar amsa a Jarrabawar. Jami’ar ta bayyana haka ne ga Manema labarai a jiya Laraba.

Hukumar Jarrabawar tace dalilin da ka jawo haka shine rashin shiri da kayan aiki da dalibai makafin suka rasa. An kira Gwamnati ta dage wajen harkar ilmin nakasassu da marasa karfi. Idan har Gwamnati ta sa karfi, ba shakka irin wannan dalibai suna da baiwar karatu, Inji ta.

Kwanan aka samu labarin wata mata da tayi shekaru 30 tana sana’ar abinci, da haka ta biyawa dan nan na ta kudin makaranta. Tun daga Ajin Nursery har ya kammala Sakandare inda ya rubuta jarrabawar WAEC. Wannan yaro dai yace uwar sa ce uban sa.

[NAIJ Hausa]





Wednesday, December 28, 2016

An kama wani babban Dan ta’addan Duniya a Najeriya


...Tuni har Obama ya kira Shugaba Buhari

– Jami’an Hukumar DSS tayi wani babban kamu


– An damke daya daga cikin manyan ‘Yan ta’addan Duniya a Najeriya


– Yanzu haka Barrack Obama ya kira Shugaba Buhari a waya




Hukumar DSS ta damke daya daga cikin manyan ‘Yan ta’addan Duniya a cikin Kasar nan. Har yanzu dai ba a bayyana suna ba saboda ana cikin bincike. Wannan mutumi da aka kama shine na uku a jerin ‘Yan ta’ddan Duniya gaba daya.

Kwanakin nan ne kuma Hukumar ta liken asiri ta gano wani yunkuri na kai hari a Kasar Amurka.  Jaridar The Nation ce dai ta bayyana wannan labari; tace an kama Babban Dan ta’addan Duniya a cikin Kasar nan.

Ana zargin wannan Dan ta’adda da kashe mutane a Duniya daga shekarar 2012 zuwa ta 2013. Yanzu haka dai Jami’an tsaro daga ko ina a Duniya sai barkowa suke yi cikin Kasar domin su gana da wannan Dan ta’adda suyi masa tambayoyi.

Ba a dai ba da sun aba har yanzu saboda halin bincike. Tuni dai har Shugaban Kasar Amurka ya kira Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya domin jin yadda abin ya faru.


EFCC: Gwamna zai maido abin da ya wawura



– Tsohon Gwamnan Jihar Gombe, Danjuma Goje na shirin maido wasu makudan kudi ga Hukumar EFCC


– Gwamnan da Sanata ne a yanzu yana neman a sasanta da Hukumar EFCC


– Sai dai Hukumar tace fa sai an  yi aman abin da aka ci




Tsohon Gwamnan Jihar Gombe kuma Sanata a yanzu, Alhaji Danjuma Goje zai maido akalla Naira Miliyan 40 daga cikin kudin da ake zargin ya yi awon gaba da su. Sanata Goje da wasu Mutane hudu suna hannun EFCC bisa zargin sama da wasu kudi har Naira Biliayan 25.

Cikin wadanda ake zargi akwai wanda ya kasance mai kai abinci Gidan Gwamnati a lokacin Goje yana Gwamna; Alhaji Sabo Muhammad Tumu. Akwai Alhaji Aliyu El-Nafaty da wani Dan Kasuwa; M. Dokoto.

Ana dai zargin Tsohon Gwamnan da karkatar da wasu kudin kwangila da na ‘Yan Majalisu. An dai dauki shekaru fiye da biyar ana shari’ar. Jaridar The Nation tace Hukumar EFCC na neman Tsohon Gwamnan yayi aman kudin, sai dais hi yana rokon alfarma, ayi ta-ta kare a wajen Kotu.

Kwanan nan kuma ana ta samun wasu bayanai masu cin-karo da juna a game da Majalisar Dattawar da kuma Ibrahim Magu na EFCC. Daya daga cikin Sanatocin Kasar yace ba gaskiya bane ace Majalisar ba ta amince da Ibrahim Magu ba a matsayin Shugaban Hukumar EFCC. Ana dai zargi akwai wasu da ke kokarin ganin bayan Magu na EFCC din.





Gobara ta kona kasuwar Gombe



Gobarar wuta ta ci kasuwar Gombe


Cikin dare wannan wuta ta tashi


Shaguna kusan 50 sun kone; an tafka asara da dama





Gobarar wuta tayi barna a Tsohuwar kasuwar Garin Gombe, inda tayi sanadiyyar rashin makudan kaya. Wutar ta tashi ne cikin dare wanda ta ci kusan shaguna 50. Yanzu dai akalla an yi rashin kaya na sama da Naira Miliyan 40.

Jaridar Daily Trust ce ta kawo rahoton. An ce wutar ta fara ci ne kimanin karfe 1 na tsakar Dare. Ana tunani igiyar wuta ce ta jawo wannan barna a lokacin da aka maido wutar lantarki. Wadanda abin ya fi shafa dai suna masu kayan kwalliya da kuma teloli.

Shugaban ‘Yan kasuwar, Alhaji Muhammad Abba Aliyu ys bayyanawa Hukumar Dillacin labarai na Kasa cewa shaguna kusan 48 ne suka kone. Alhaji Muhammad yace yayi asarar kaya na sama da Naira Miliyan 2.

Wani Dan kasuwar yace yana ji, yana gani, shagon sa ya kone. Yace sun iso ne wajen karfe 3 na Dare; lokacin tuni wutar ta dade da fara ci. Ya dai bayyana cewa ya rasa abin da ya fi Miliyan 2. Akwai wani Inyamuri, Chibeza Raymond da yake da Shaguna har biyu, yace yayi asarar sama da Naira Miliyan 7.


[NAIJ Hausa]


Tuesday, December 27, 2016

Ashe ‘Yan Shi’a suna Bikin Kirismeti



‘Yan Shi’a sun yi Bikin Kirismeti tare da Kirista


– An ga Mabiya Shi’a a Coci tare da Kiristoci suna taya su murna


Mabiya Shi’a sun kuma aika katin taya murna ga Kirisoci




‘Yan Shi’a sun taya Kiristoci murnar Bikin Kirismeti wannan shekarar a Garin Kaduna. An dai ga Mabiya Shi’a da dama a cikin Coci tare da Kiristooci yayin da ake Bikin Kirsmetin wannan shekara.

Har da wani kati kuma ‘Yan Kungiyar IMN ta Shi’a ta aika domin taya Kiristoci murnar wannan Idi. A kan yi Bikin Kirismeti na a Ranar 25 ga Watan Disamba da cewa a Ranar ne aka haifi Yesu.

A Kasashe irin su Iran, tuni dama an dade ‘Yan Shi’a suna shiga Coci domin su taya Kiristoci Kirismeti. Sai gas hi wannan abu ya faru wannan karo a Garin Kaduna, hakan dai y aba kowa mamaki.

A baya dai Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa daga yanzu babu wani tattaki ko gangamin da ya sabawa doka a Jihar. Gwamnatin tayi wannan ne domin kawo karshen lamarin ‘Yan  Kungiyar IMN na Shi’a a Yankin da ta kira masu tada zaune tsaye.



Kaduna: ‘Yan Shi’a sun yi Bikin Kirismeti tare da Kirista a Coci


[NAIJ Hausa]



Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...