Monday, February 13, 2017

'Yar autar Buhari ‘Hannan’ mai daukar hoto


– Ko ka taba ganin Diyar shugaba Muhammadu Buhari Hannan


Hannan ita ce ‘yar autar Baba Buhari


Hannan Buhari tana sha’awar daukar hotuna




Wasu hotunan diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari sun bayyana a shafin gizo. An dai ga ‘yar autar shugaban kasan a wani hoto rike da ‘kemera’ abin daukar hoto. Hannan din dai mai shekara 18 tana da sha’awar daukar hoto.  



Hannan Muhammadu Buhari ta dauro hoton ne a shafin ta a cikin bakin launi. Sai dai masu bin Diyar shugaban kasar a yanar gizo sun tofa albarkacin bakin su a game da hoton. Jama’a dai suna cewa Diyar shugaban kasar tana da dan-karen kyau.


Sai dai wani daga cikin masu-bin Diyar shugaban kasar ya ba ta shawarar cewa bai dace ta saka bakin hoto ba, watau kamar ana wani makoki. Ana dai ta rade-radin cewa shugaba Buhari na kwance a Landan bai da lafiya.




Hannan da kemarar ta

[NAIJ Hausa]

1 comment:

  1. Allah Ya ba baba lafia. Hausawa Na cewa kowa da sana'ar da ta karbe shi... Hannan Allah YA ba da sa'a.

    ReplyDelete

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...