–
Babban Malamin Duniya Mufti Menk ya goyi bayan Sarki Sanusi II
– Sarkin
Kano yace za a hana talaka yawan aure a kasar sa
–
Malamin yace Sarkin Kano yayi daidai kuma ‘Yan Jarida ba
su kyautawa
Babban malamin Duniya mai fatawa Sheikh Ismail Menk ya
goyi bayan Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a game da maganar cewa za a hana
talaka tubus kara auren mata a kasar sa. Kalamai da kudirin na Sarkin Kano sun
jawo ce-ce-ku-ce a Gari.
Mufti Menk ya nuna goyon bayan sa ga yunkurin Sarkin
yace dama can aikin Hukuma ne ta duba yadda ake gudanar da al’umarra ta kuma
kawo gyara. Malamin yace ‘Yan Jarida ne ke kara hura wutar maganar inda suke
nuna cewa Sarkin na nema yayi fada da Sunnar Manzon Allah SAW.
Babban Shehin na kasar Zimbabwe yace ko da cewa aure
Sunnah ne mai karfi, amma ko Manzon Allah SAW cewa yayi wanda yake da hali
yayi, wanda kuma ba sa da shi sai ya hakura, ina kuma maganar karawa.
Malamin yace hakan zai kawo gyara a harkar aure inda
za a mutunta darajar ‘ya ‘ya da kuma mata. A wata hira da Hukumar dillacin
labarai na kasa watau NAN tayi da wasu mata a Maiduguri, wasu sun bayyana cewa
hakan abu ne mai kyau yayin da wasu suka yi tir da batun.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment