– Gwamna Ayo Fayose na Jihar Ekiti
yace in dai aka zo fannin siyasa to ya kai Farfesa
– Ayo Fayose yace an dade ana
gwabzawa da shi, shi kada ne ba ya jin tsoron shugaba Buhari
– Kuma Gwamna Fayose yace an nuna masa wata rana zai mulki Najeriya
Gwamnan
Jihar Ekiti Ayodele Fayose yace idan aka shigo fannin siyasa ya kai matasayin
Farfesa. Gwamna Ayo Fayose yace shi hukuma ce mai zaman kan ta idan dai ana
maganar siyasa a cikin Kasar nan.
Ayo
Fayose yace an dade ana bugawa da shi tun ba yau ba. Gwamna Fayose yace kowa
dai ya buga ya bar sa. Gwamnan yace shi kadai ne ba ya jin tsoron Buhari don
kuwa babu irin sa. Fayose yace yayi Gwamna lokacin Obasanjo, ya kuma yi lokacin
shugaba Jonathan sannan lokacin Buhari.
Fayose
ya bayyana haka ne a wata hira da yayi da Jaridar Punch. Fayose yace ko ‘Yan
Jam’iyyar APC sai dai su shafa masa lafiya don kuwa ya kai Farfesa a fagen
siyasa. Daga baya ma dai mun samu labarin Gwamnan yace an nuna masa cewa zai
mulki Kasar nan.
Kwanan
nan Gwamna Fayose ya kira Gwamnatin tarayya ta kara kudin masu bautar Kasar
zuwa N50, 000. Gwamnan ya nemi a karawa matasan Kasar albashi don kuwa yanzu N
19, 8000 babu inda za ta.
No comments:
Post a Comment