– Kasar
Amurka za ta saka kudi wajen harkar wutan Najeriya
– Amurka
na shirin kashe dala biliyan 1 a Najeriya domin ganin an samu wuta
– Idan
har hakan ta yiwu za a daina dauke wutar lantarki a Kasar
Kasar Amurka na shirin kashe
makudan kudi domin ganin Najeriya ta samu wutar lantarki tsayayye. Amurka dai
za ta cigaba da kokari a kan harkar wutar lantarki a Nahiyar Afrika domin ganin
an fita daga duhu.
Amurka na shirin saka kudi
har dala biliyan guda a Najeriya domin gyara wutar lantarki. Tun ba yau ba dai
Kasar ta saba taimakawa Najeriya. Asali ma dai an kashe makudan kudi daga
shekarar 1999 zuwa yau amma har yanzu babu tsayayyen wutar lantarki a Najeriya.
Kamar yadda Jaridar The
Nation ta rahoto, Mista Andrew Herscowitz wanda shi ne mai kula da Kwangilar Power Africa ya bayyana haka a wani
taron karawa juna sani da aka yi a Abuja. Idan har aka samu karin mega watta
30, 000 tabbas za a daina dauke wuta a Najeriya.
[NAIJ Hausa]
Shu Shugaban kasar amuruka da ya ce baya san bakakin mutanen, me ya hada shi da taimaka masu? Ya rike taimakon shi
ReplyDelete