– Wata
Amarya ta rasu makonni uku bayan an daure mata aure
– Amaryar ta rasu tana da juna biyu
– Asali
ma dai ta rasu ne bayan nakuda
Wani abin tausayi ya faru kamar yadda muka karanto a shafin Facebook. Wata Amarya dai tace ga garin ku nan, duka-duka ba ayi wata guda da yin auren ta ba. Wannan Amarya dai ta rasu jim kadan bayan an daura auren ta.
Wata kawar Amaryar mai suna Princess Nkiru ce ta bayyana
haka yayin da ta ke mata ta’aziya a shafin ta na Facebook. Nkiru Momah tace
dama can Amaryar tana da juna biyu, sai ga shi ta cika wajen haihuwar ‘da.
Kawar Marigayiyar tana mai kokawa da jimami da ce: ‘Dama na
kwarai ba su dadewa.’ Har yanzu dai tana jin abin kamar a mafarki. An daura
auren wannan Budurwa mai shekaru 23 a Watan Disamba, ta kuma haihu a Ranar 11
ga Watan Junairu, sai dai jim kadan bayan nan ta ce ga garin ku nan.
Haka kuma kwanaki dai wani Ango daga Garin Katsina ya rasu
shi ma ba a dade da daura auren sa ba. Allah ya bada ikon hakuri.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment