– An gano maganin cutar nan ta
Kanjamau a wata Jami’a da ke Najeriya
– Farfesa Maduike Ezeibe na Jami’ar Michael Okpara ta
Jihar Abia yayi wannan bincike
– Shugaban
Makarantar ya bayyana haka a jiya
Idan dai ta tabbata Najeriya za tayi kudi da wannan magani
Bayan shekara da shekaru ana
bincike wani Farfesa mai suna Maduike Ezeibe a Jami’ar koyon aikin gona ta Michael Okpara ya gano maganin cutar
nan da ta gagari mutane watau Kanjamau. A Turance kuma ana kiran ta HIV wanda
ke zama AIDS idan ta rika.
Shugaban Jami’ar da ke Garin
Umudike na Jihar Abia ya bayyana haka bayan ya tara manema labarai. Farfesa Francis
Otunta yayi ikirarin cewa wani Malamin Makarantar ya gano maganin cutar da ke
karya garkuwar jiki.
Farfesa Maduike Ezeibe da
yayi wannan bincike dai yayi bayanin matakan da ya bi, da kuma sakamakon da ya
samu. Yayi amfani da sinadarin Aluminium
Silicate da kuma Magnesium Silicate.
Sai dai abin da ban mamaki musamman dai tun da Farfesa Ezeibe Likitan dabbobi
ne, ita kuma Kanjamau garkuwar jikin Dan Adam ta ke karyawa.
Kwanaki Jaridar Huffington
Post ta rahoto cewa yanzu haka an samo maganin Kanjamau kuma har an yi wa wani
ma’aikaci a Kasar Birtaniya magananin wannan cuta, kuma ya warke.
[NAIJ Hausa]
ALLAH YAQARA KAWO MAFITA
ReplyDeleteDAN ALLAH YI GAGGAWAR FIDDA MAGANIN HIV
ReplyDeleteDOMIN JAMA A NA CIKIN WANI HALI
OUT MEDICINE HIV EMERGENCY PLEASE
DAN ALLAH ATAUSAYA WA RAYUWA