– Shugabannin kasar Amurka sun sha ban-ban da na Afrika
– Barrack Obama da mataimakin sa Biden sun bar kujera ba
su da gidan kan su
– Joe Biden a jirgin kasar haya ya karasa gida bayan ya sauka
Shugabannin
Afrika dai sun matukar sha ban-ban da takwarorin su na sauran kasashen Duniya.
Kwanan nan aka nemi wasu motoci a Kasar Ghana bayan shugaban kasar ya bar mulki
aka rasa. A kasar Amurka kuwa ba haka lamarin yake ba.
Bayan
shugaban kasar Amurka Barrack Obama ya sauka daga mulki bai wuce ko ina ba sai
gidan haya. Haka kuma Mataimakin sa Joe Biden wanda ya fi shekaru 35 a
Majalisar Dattawa na kasar kafin ya zama Mataimakin shugaba Obama na shekaru 8.
Biden
dai a jirgin kasa na haya ya koma kauyen su na Garin Wilmington inda ya koma ko
gidan kan sa bai mallaka ba. A Najeriya dai kuwa duk wanda ya rike matsayi bai
sace kudin al’umma ba ma kamar ya zama wani sakarai ne.
Yau ne Donald Trump yayi
waya da shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda yayi alkawarin taimkawa Najeriya wajen fada da Boko Haram. Trump din ya nemi ganawa da Buhari nan gaba.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment