– Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori Sojojin da ke masa gadi
– Da alamu dai an samu baraka ne ta hannun Sojojin
– Kamar yadda aka saba Jami’an DSS
za su cigaba da kare shugaban kasa
Shugaban
kasa Muhammadu Buhari duk ta kare ya salami Sojojin da ke gadin sa ya kuma maye
gurbin su da Jami’an DSS kamar dai yadda aka saba a baya. Ba mamaki an samu
matsala ne ta wajen Sojojin da ke gadin na sa.
Jaridar
The Nations tace daf da shugaba Buhari zai tafi Landan ya bada wannan umarnin
ya nemi Sojojin da ke gadin sa su bar fadar shugaban kasar. Asali dama can
Jami’an DSS ne ke aikin kare shugaban kasa da iyalan sa.
Farkon
hawan shugaban kasa Buhari ya kori Jami’an DSS da ke gadin shugaban kasa ya
dauko Sojoji a matsayin su. Hakan dai ya kawo matsala tsakanin dogarin shugaban
kasar Kanal Abubakar Lawal da kuma shugaban masu kare sa Abdulrahman Mani. Har
daga karshe dai shugaba Buhari ya salami Mani daga aiki, sai dai yanzu kamar an
koma gidan jiyar.
No comments:
Post a Comment