Tsugune
ba ta kare ba: An kara kama tsohon Gwamna kafin ya bar Kotu
– Hukumar EFCC ta dai rutsa tsohon Gwamnan Katsina Barista Shema
– Da alamu EFCC ta kara damke Shema da wani sabon laifi
kafin ya bar Kotu
– Ana binciken tsohon Gwamnan da laifin satan kudin
al’umma
Tsohon Gwamnan Jihar Katsina
Barista Ibrahim Shema dai yana ganin ta kan sa. Don kuwa da alamu Hukumar EFCC ta
kara damke sa bayan an tashi daga wata shari’a da aka yi da shi a kotu kamar
yadda Jaridar Daily Trust ta rahoto.
Yayin da ake shirin barin
kotun, Jami’an Hukumar EFCC suka dura motar tsohon Gwamnan suke nemi ya biyo
su, su ka kuma tuka motar sa a baya. Jaridar Daily Trust ce dai ta kawo duk
abin da ya faru. Mai magana da yawun tsohon Gwamnan dai yace ba kama sa aka yi ba, tuni dai an daga shari'ar sai nan da mako kusan biyu.
Dama can Hukumar EFCC ta
nemi a kama tsohon Gwamnan a rufe a gidan yari, hakan zai sa ba za a neme sa a
rasa ba a ko da yaushe. Jami’an ‘Yan Sanda dai sun kora Jama’a da ke kokarin
zagaye kotun.
Tun
kwanaki dai aka gurfanar da Tsohon Gwamnan na Jihar Katsina Barista Ibrahim
Shehu Shema a gaban Babban Kotun Jihar da ke cikin Garin Katsina. Shema ya zargi
Gwamnatin APC da makarkashiya, sai dai Gwamna Masari yace Shema ya ji da kan
sa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment