– Wani
matashi ya kashe kan sa Garin Kano
– Wannan abu ya faru ne a Karamar Hukumar Gezawa
– Ko
me ya kawo wannan? Duniya ce ta masa zafi
Mun samu labara daga Jaridar
Daily Trust cewa wani matashi ya rataye kan sa har Lahira a Garin Kano. Har
yanzu dai ba za a iya cewa ga dalilin da ya sa wannan matashi ya aikata wannan
mugun abu ba.
An dai gane wannan matashi
mai suna Nura kuma har a lokacin da aka samu wannan labari kafafun sa na lilo a
bisa bishiyar sa ya rataye kan sa. Matashin ya rubuta sunan sa ne a wurin kafin
ya kashe kan san.
Wannan abu dai ya faru ne a Garin
tsamiya da ke cikin Karamar Hukumar Gezawa na Jihar Kano. Wanda yake wurin yace
babu wanda ya san mai yayi wa wannan matashi zafi, sai dai aka iske gawar sa
tare da casbaha da riga da wasu komatsen sa.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment