– Duk da yawan Jama’an Arewacin
Najeriya Yankin ya fi ko ina talauci inji masu nazari
– Ana fama da matsalar almajirai a Arewacin Najeriya
– Ga yawan mace-macen aure
“Matukar
a arewa da karuwai,
yan
daudu dasu da magajiya.
Da
samari masu ruwan kudi,
Ga
mashaya can a gidan giya.
Matukar
yayan mu suna bara,
Titi
da Loko-lokon Nijeriya.
Hanyar
birni da na kauyuka,
Allah
baku mu samu abin miya.
Sun
yafu da fatar bunsuru,
Babu
mai tanyonsu da dukiya.
Babu
shakka yan kudu zasu hau,
Dokin
mulkin Nijeriya.
In
ko yan kudu sunka hau,
Babu
sauran dadi, dada kowa zai
sha
wuya.
A
Arewa zumunta ta mutu,
Sai
karya sai sharholiya.
Camfe-camfe
da tsibbace
tsibbacen,
Malaman
karya yan damfara.
Sai
karya sai kwambon tsiya,
Sai
hula mai annakiya.
Ga
gorin asali da na dukiya,
Sai
kace dan annabi fariya.
Jahilci
ya ci lakar mu duk,
Ya
sa mana sarka har wuya.
Ya
sa mana ankwa hannuwa,
Ya
daure kafarmu da tsarkiya.
Bakunan
mu ya sa takunkumi,
Ba
zalaka sai sharholiya.
Wagga
al’umma mai zata yo,
A
cikin zarafofin duniya.
Kadan
kenan daga cikin matsalolin Arewa daga wakar Marigayi Sa’adu Zungur a game da Arewa. Arewa dai
na fama da matsaloli rututu. Ko da
Arewa ta ciri tuta wajen yawa haka kuma ta ciri wata tutar wajen yawan
mace-macen aure da jahilcin tsiya da yayi mana katutu ta ko ina ban da kuma
talauci.
Domin
kawo karshen wannan matsala a Yankin Arewa dai dole a komawa Ubangiji da farko.
Jama’a sun kara lalacewa fiye da tunani sam babu tarbiya. Duk al’ummar da mai
kudi ya zama shi ke fada-a ji, to ta shiga cikin babbar matsala. Ya zama dole a
komawa Ubangiji wajen komai daga kasuwanci a shago zuwa rayuwar aure a gidajen
mu.
Ya
zama dole kamar yadda Mawaki yace, Arewa mu so juna. Dole Arewa ta so ‘Yan uwan
ta, ta kuma zauna lafiya ba tare da rikici ba, idan har ba mu yi ba, za a
cigaba da yi mana dariya. Kowa dai ya san yadda su Sardauna su ka zauna da
abokan zaman na su.
Kai
Bahaushe ba shi da zuciya ,
Zaya
sha kunya nan duniya “.
“Mu
dai hakkin mu gaya muku,
Ko
ku karba ko kuyi dariya.
Dariyar
ku ta zam kuka gaba,
da
nadamar mai kin gaskiya.
Gaskiya
ba ta neman ado,
ko
na zakin muryar zabiya.
Karya
ce mai launi bakwai,
ga
fari da baki ga rawaya.
Ga
kore ga kuma algashi,
toka-toka
da ja sun garwaya”.
[Marigayi
Sa’adu Zungur a cikin waken sa mai suna “Arewa Jamhuriya ko Mulukiya”.]
Ya
kuma zama dole ‘Yan Arewa su cire girman kai da kasala su nemi na su. Kai in
dai Dan Arewa na nan da bambadanci da roko da tumasanci ba za mu taba cigaba ba.
Wannan kyashi shi ya ke kawo bakin ciki da hassada a cikin mu. Haka kuma masu arziki su daina rowa, sai a zama daidai.
Bugu
da kari kuma dole Mutanen Arewa su yi ilmi; ilmin boko da na Arabi. Idan kuma
an yi Ilmi sai ayi aiki da shi, ga masallatai amma babu imani a zukata. Dole Mutan Arewa mu san Ubangiji da kuma hanyar
lomar mu, za a ga amfani Duniya da lahira.
Muhammad Malumfashi ya rubuta wannan a shafin NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment