– Jami’an
‘Yan Sanda sun damke wasu daga cikin masu tada rikici a Kudancin Kaduna
– Yanzu
haka an kama mutane kusan 17 wanda suna hannun Hukuma
– Za
a gurfanar da masu laifin a Kotu
Hukumar ‘Yan Sanda ta samu
nasarar damke wasu daga cikin masu hannu a rikicin Kudancin Kaduna. ‘Yan Sanda
dai sun kama mutane 17 da manyan makamai kamar kuma tuni za a wuce da su Kotu
bayan an gama tsare su.
Kakakin ‘Yan Sanda na Kasa,
Jimoh Mashood yace Hukumar tayi nasarar kama wadanda ake zargi, ta kuma tsare
su inda tayi masu tambayoyi, ana kuma kammala bincike za a maka su a gaban Kotu
kamar yadda Premium Times ta bayyana.
Sunayen wadanda aka kama sun
hada da: Magaji Shu’aibu, Abdulkareem Abdul, Goma Adamu, Danlami Yakubu,
Danjuma Barde, Idris Bello, Adamu Haruna, Suleiman Saleh, Adamu Umar, Abubakar
Muhammad, Bulus Jatau, Nelson Paul, Hassan Idris, da sauran su.
Jami’in ‘Yan Sandan yace za
a gurfanar da su da laifin daukar makamin da bai hallata ba, tada zaune-tsaye
da ma sata. An dai same su da manyan makamai kusan 29.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment