– Dubun
dubatar mutane suna nema a tsige shugaba Trump na Amurka
– Mutane sama da 650, 000 suna goyon bayan an tsige
Donald Trump
– Shugaba Trump dai na ta kara rasa
farin jini
Mutane
sama da 650, 000 su ke yunkurin ganin an tsige shugaban kasar Amurka Donald
Trump daga kujerar sa. Amurkawa dai na ta kara nuna rashin goyon bayan su da
sabon shugaban na su Donald J. Trump.
Tun
ranar da Trump yah au mulki dai aka fara shirin ganin an sauke sa. Kungiyoyi da
dama irin su RootsAction da FreeSpeech suka tashi tsaye wajen ganin Trump ya
bar Gidan White House. Yanzu haka dai
an samu mutane 655, 363 da suka yi mubaya’a da a tsige Trump.
[NAIJ Hausa]
Ai gwara a tsige shi. Hakan ya fi dacewa da shi.
ReplyDelete