Wednesday, February 8, 2017

Ko ni ba na magana da Buhari...-Inji Femi Adesina




– Mai magana da bakin shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi karin haske


– Femi Adesina yace ko shi bai yi magana da Buhari ba a Landan


– Sai dai Adesina yace yana zantawa da na-kusa da shugaban kasa




Mai magana da bakin shugaban kasa Femi Adesina yayi karin haske game da rashin lafiyar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ke Landan tare da kuma bayani a kan ranar da shugaban zai dawo. Jaridar Sahara Reporters dai tace Buhari na iya kara watanni hudu nan gaba a Landan.

Femi Adesina a wata hira da yayi a talabijin yace ko shi kan sa bai yi magana da shugaban kasar ba, sai dai ya kan yi magana da na-kusa da shi din. Adesina yace yak an tattauna da wadanda suke tare da shugaba Buhari a can Landan.

Mai magana da bakin shugaban kasar yace shugaba Buhari zai dawo kafin ma lokacin da ake tunani. Adesina ya kuma soki wasu da ke ta kara ruruta maganar tare da daura laifin tabarbarewar kasar bisa kan tsohon shugaba Jonathan.

Babban Lauyan nan na kasa Femi Falana SAN ya soki shugaba Muhammadu Buhari game da al’amarin rashin lafiyar sa. Falana yace ya kamata ace ‘Yan Najeriya sun san halin da shugaban su yake ciki.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...