Friday, February 24, 2017

Osinbajo zai gyara tattalin arzikin Najeriya a wata 2





Mukaddashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya shirya farfado da tattalin arzikin Najeriya cikin watanni biyu. Najeriyar dai ta samu durkushewar tattalin arziki a a bara.


Farfesa Osinbajo ya kulla niyyar shawo kan matsalar tattalin arzikin Najeriya cikin kankanin lokaci. Shugaban rikon kwaryar dai zai cin ma wannan burin ne ta hanyar saukake harkar kasuwanci a kasar.

Yanzu haka an nada wani kwamiti wanda shi mukaddashin shugaban kasar yake jagoranta mai suna PEBEC wanda zai kawo sa’ida wajen harkar kasuwanci a Najeriya. Hakan zai taimakawa kananan ‘yan kasuwa na kasar ya kuma habaka tattalin arziki cikin kwanaki 60. Ana so dai duk wani dan kasuwa da zai zo Najeriya da hajar sa ya kammala kamai cikin ‘yan sa’o’i.

Jiya ne shugaban rikon kwaryar ya dura filin jirgin saman Legas ba tare da tsammani ba inda ya rika bincika abubuwa da kan sa. Gwamnati na kokarin ganin Najeriya ta shiga sahun kasar da kasuwanci ya ke da sauki ba tare da wahala ba, wannan zai taimakawa tattalin arzikin kasar.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...