Thursday, February 9, 2017

Ga wata jarumar mace mai yaki da ‘Yan Boko Haram


Aisha Gombi mai kamar maza tayi kaurin suna wajen fada da Boko Haram


– Ga wata jarumar mace mai yaki da ‘Yan Boko Haram


– Aisha tace ‘Yan Boko Haram tsoron ta su ke





Makashin maza: Ga Aisha dodon ‘Yan Boko Haram



Jaridar Guardian ta dauko wani rahoto a game da wata mace mai kamar maza. Aisha Gombi dai mafarauciyar barewa ce a da, yanzu kuwa ta rikide farautar mayakan Kungiyar Boko Haram, kuma tayi kaurin suna don kuwa sun san ta. Aisha tana da shekaru 38 a Duniya.

Kwanaki da ‘Yan Boko Haram suka sace wasu yara ai sai kawai sai Sojoji suka dankarawa Aisha waya. Nan take ta shirya mafarauta aka shiga Dajin Sambisa. Dama can a kusa da dajin sambisa aka haifi Aisha Gombi Bakari ta kuma saba fita farautar manyan dabbobi tare da kakan ta.




Aisha tace su kan su ‘Yan Boko Haram suna shakkar ta don kuwa ta saba kubutar da mutane daga hannun su. Aisha tana da bataliya inda ta ke jagorantar kattin maza wajen kubuto da wadanda ke hannun ‘Yan Boko Haram. Ba mamaki tana cikin wadanda aka dauka aikin soji a bara.




An dauko wannan labari daga Guardian aka fassara aka buga a NAIJ Hausa

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...