Monday, February 13, 2017

Patience Jonathan za ta tsaya takarar Sanata



– Tsohuwar Uwargidan Najeriya Patience Jonathan za ta tsaya takara


Madam Patience Jonathan za ta nemi ta tsaya takara a zaben 2019


Watakila Misis Jonathan za ta tsaya takarar Sanata



Da alamu tsohuwar uwargidan Najeriya Madam Patience Jonathan za ta nemi tsayawa takara a zabe mai zuwa. Mijin na ta Dakta Goodluck Ebele Jonathan dai yayi mulki na shekaru biyar a kafin Muhammadu Buhari ya kada sa a zabe.

Patience Jonathan na shirin neman kujerar Sanata na Jihar Ribas a zabe mai zuwa na 2019 kamar yadda mu ke samun labari. Wannan labari dai ya jawo ka ce-na ce daga bakin mutane da dama na Kasar.

Misis Jonathan na iya tsayawa takarar kujerar Sanatar Mazabar Gabashin Jihar Ribas. Asali dama Madam Jonathan mutumiyar Jihar Ribas din ce. Idan dai har tsohuwar Uwargidan ta tsaya takarar, ba mamaki za ta samu nasara, don ko Gwamnan Jihar mutumin ta ne.

Idan ba a manta ba can Jam’iyyar APC ta kai karar Madam Jonathan din a gaban Kotun Duniya ICC. APC tace Uwargida Patience Jonathan tayi kokarin tada rikici yayin yakin neman kujera da kalaman ta a wancan lokaci na zaben shekarar 2015.



[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...