Tuesday, February 14, 2017

Dan wasan Najeriya ya fadi ya mutu a filin kwallo


Wani Dan wasan Najeriya ya fadi ya mutu a filin kwallo


– Dan wasa Henry Obiekwu ya mutu ana tsakiyar wasa


– Marigayin ya kasance yana bugawa Kungiyar Enugu Rangers




Kwallon kafar Najeriya dai ta gamu da abin takaici bayan da wani Dan wasan Kungiyar Enugu Rangers na gida ya fadi matacce ana tsakiyar wasa jiya Litinin 13 ga wannan wata. 

Tauraron Dan wasan Henry Obiekwu ya kwanta dama ne a jiya bayan ya buga wani wasa na kawance tsakanin Kungiyar ta su da ta Samba FC. Dan wasan yayi kukan ciwon kirji hakan ta sa aka cire sa daga wasan.

Dan uwan dan wasan wanda ya kuma taba bugawa Super Eagles Kingsley Obiekwu ya tabbatar wa Africanfootball cewa dan uwan na sa Henry ya rasu. An dai yi kokarin wucewa da dan wasan Asibitin Eastern Nigeria Medical Centre a Birnin Enugu inda a can ya ce ga garin ku.
A Ingila kuma wasu tsageru sun kai hari gidan wani dan wasan Liverpool saboda jin haushin ya zubar da finariti a Gasar cin kofin nahiyar Afrika. Dan wasa Mane ya barar da bugun daga kai sai mai tsaron gida Gasar AFCON, wasu suka ce da gan-gan yayi hakan.


[NAIJ Hausa]

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...