Wednesday, February 8, 2017

Bukola Saraki ya nada Hakeem Baba-Ahmed shugaban ma'aikata



– Bukola Saraki ya nada Hakeem Baba-Ahmed babban matsayi
– Daga yanzu Dr. Hakeem Baba-Ahmed ne shugaban Ma’aikatan ofishin Saraki
– Kwanakin baya mai rike da ofishin yayi murabus




Shugaban majalisar dattawa na Najeriya Dr. Abubakar Bukola Saraki ya nada Dr. Hakeem Baba-Ahmed OFR a matsayin shugaban ma’aikatan ofishin sa kamar yadda muka samu labari.
Hakeem Baba-Ahmed yayi aiki da ma’aikatu da dama na gwamnatin tarayya bayan Jihar Kaduna inda har ya kai matsayin Sakataren din-din-din. Hakeem Baba-Ahmed kuma dan boko ne wanda yayi digiri har digir-digir a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya da wasu Jami’o’in a Kasar Ingila.




Bayan nan Dr. Hakeem ya koyar a Jami’a ya kuma taba aiki da Hukumar zabe ta kasa watau INEC. A zaben da aka yi a shekarar 2015 shi ne Jami'in Jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, dama can ya taba rike shugabancin Jam’iyyar a Jihar.
Mun dai samu labarin an dauke wutan lantarki a Majalisar dattawa yayin da ake tsakar tantance wadanda za a tura a matsayin Jakadun Najeriya wata zuwa wasu Kasashen. Har wa yau an tantance Ahmad Nuhu Bammalli wanda shi ma Dan Zariya ne a matsayin Jakadan Najeriya.

No comments:

Post a Comment

Featured Post

Goron Juma'a: Falalolin Ranar Juma'a a Musulunci

Manyan faloli 3 na Ranar Juma'a mai albarka  A yau dai ta ke Ranar Juma'a wanda ba shakka ke da falala Musulmai sun dauk...