–
Kiristocin Jihar Katsina suna ta addu’a domin ubangiji ya ba Buhari lafiya
– Kungiyar
CAN dai ta fara fara
azumi da salloli domin shugaban kasar
–
Shugaba Muhammadu Buhari yana Ingila tun-tuni
A Jihar Katsina mahaifar shugaban kasa Muhammadu
Buhari Kiristoci ne suka shiga addu’o’i dare da rana domin Ubangiji ya ba
shugaban kasar lafiya. Kiristocin dai sun tashi ne da azumi da kuma addu’o’i
domin shugaban kasar ya dawo aiki.
A Jiya Litinin dai Kungiyar CAN ta Kiristoci suka
tashi da niyyar azumi har na mako guda domin Buhari. Kungiyar dai tana da ‘Ya
‘ya kusan 65,000 a Jihar Katsina. Kamar dai yadda muka samu labari daga Jami’an
NAN masu dillacin labarai.
Kiristocin za su yi addu’a ne na musamman a manyan
Cocin da ke Jihar, kamar su Cocin da ke Kofar Kaura da dai wasu da ke cikin
gari. Kiristocin suka ce addu’ar su shugaba Buhari ya samu sauki ya dawo ya
cigaba da aikin gyaran da ya faro.
'Yan Kungiyar Jama'atu Nasril Islam dai su ma sun dage da yi wa Shugaba Buhari addu'a. A Jihar Borno kuwa, sai sauke Al-Kur'ani ake yi.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment