– Wani
tsohon Fasto ya karbi Addini Musulunci a Birtaniya
– Tsohon Faston yace tun tuni hankalin sa bai kwanta da
Addinin Kiristanci ba
– Faston
yace a da bai fahimci Musulunci ba
Wani tsohon Fasto a Ingila ya
karbi addinin Musulunci ya kuma bayyana dalilin sa na barin Addinin
Kiristancin. Faston yace galibi dai Mutanen Kasar Birtaniya ba san Musulunci
ba, sai abin da aka fada a Talabijin
Tsohon Faston yace a
Talabijin ba abin da ake fada irin labarin ta’addanci da sunan addinin. Sai dai
ko da ya je Kasar Misra sai ya ga ashe ba haka Musulami suke ba. Tsohon Malamin
Cocin yace ya iske Musulmai suna da son Jama’a da kuma ibada domin su mutu, su
tafi Aljanna.
Tsohon Malamin dai ya
kasance yana koyar da ilmin addinai ne a Kasar Birtaniya wanda wannan ya wayar
masa da kai kwarai. Daga baya har ta kai ya bada aron ajin sa ana yin salla a
lokacin watan Ramadan.
Wata Rana dai ana cikin
sallah kamar yadda aka saba, shi kuwa yana ta kallon su a baya, sai aka karanta
wata aya a Kur’ani da ma’anar ta ke cewa: Idan wadanda ba su yi imani ba suka
ji ayoyin Allah, sai hawaye ya cika idanun su domin sun ji gaskiya…’ Ko da ya
ji wannan aya sai hawaye suka cika masa idanu, sai dai ya yayi ta maza gudun
dalibai su gane.
Bayan nan ne wannan mutumi
ya tafi babban masallacin Birnin Landan ya karbi Addini Musulunci wajen wani
tsohon mawaki wanda ya zama Malami a yanzu Yusuf Islam bayan ya fahimci
Musulunci.
An tsinkayawo wannan labara daga
shafin aboutislam.net, na kuma fara bugasa a NAIJ Hausa
No comments:
Post a Comment