– Bayern
Munich ta tarwatsa Arsenal a Gasar Champions League
– Wasu suna ganin ya kamata Koci Wenger ya bar Arsenal
– Manyan ‘Yan wasa na iya barin
Kungiyar
Kocin
Kungiyar Arsenal watau Arsene Wenger na fuskantar barazana da kalubale bayan
Kungiyar sa ta kwashi kashin ta a hannun Bayern Munich shekaran jiya. Bayern
Munich din dai ta koyawa Arsenal darasi da ci 5-1.
Wasu
suna ganin ya kamata Kocin ya tattara kayan sa ya bar Kulob din don kuwa duk
shekara Arsenal din ba ta kai ko ina a Gasar. Wannan ne dai shekara ta 6 da ake
yi waje da Arsenal din a wannan zagayen.
Arsenal ta kwashi kashin ta a hannu
An
samu rahoto cewa dan wasan gaban Kungiyar Lucas Perez na shirin tashi ya bar
Arsenal din saboda karancin buga wasanni. Da alamu dai Manyan ‘Yan wasa irin su
Alexis Sanchez ba za su cigaba da taka leda a Kulob din ba.
Haka
Kungiyar Barcelona ta sha dan banzan kashi hannun Kungiyar PSG ta Faransa a
Gasar na UEFA Champions League. Kungiyar
PSG din dai tayi wa Barcelona kaca-kaca ne a filin wasan ta da ke Garin Paris.
An fara tunani za a maye gurbin Koci Luis Enrique da Ronald Koeman.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment