– An
sace wasu baki ‘Yan wata kasa a Najeriya
– Bakin da aka sace dai mutanen kasar Rasha ne da Kasar
Ukraine
– Wannan abu ya faru ne a Yankin Neja
Delta
Mun
samu labari cewa an sace wasu baki ‘Yan kasar waje a cikin Najeriya. Wannan
abin kunya dai ya faru ne a Yamkin Neja-Delta mai arzikin mai a kasar.
An
dai sace har mutane 7 wadanda duk ‘Yan kasar Rasha ne sannan kuma da wani mutum
guda tak dan kasar Ukraine mai makwabtaka da Rasha. ‘Yan fashin kan teku ne dai
suka sace bakin a kusa da Garin Brass da ke Yankin Kudu-maso-Kudu na Kasar.
Kafar
yada labarai na kasar Rasha mai suna TASS ta sanar da wannan labari. ‘Yan
fashin kan tekun dai sun kai hari ne ga kirgin da ya kwaso ‘Yan kasar Rashan a
wani Yanki mai arzikin mai. An yi musayar wuta tsakanin ‘yan fashin da masu
gadin jirgin. Jami’an Soji dai ta maida martani kwakkwara game da harin.
No comments:
Post a Comment