–
Naira tayi tashin da ba ta taba yin irin sa ba
– A
cikin ‘yan kwanakin nan dai Naira tana kara mikewa
Da alamu hakar babban bankin Najeriya na CBN za ta ci wa ruwa don
kuwa har abubuwa sun fara yin kyau. Kwanan nan ne dai babban bankin kasar watau
CBN ya sauya tsare-tsaren sa na harkar kudin kasar.
Makon jiya dai sai da Nairar tayi irin dukan kasar da ba ta taba
yi ba, don kuwa an wayi gari an samu Dalar Amurka tana kan Naira 520, Tun da
ake ba a taba samun lokacin da Naira ta fadi war-was kamar haka ba.
Yanzu haka dai ana sayar da Dalar Amurka a kan N470 wanda an samu
ragin kusan N50 kenan cikin ‘yan kwanaki biyu. Babu dai lokacin da Naira tayi
irin wannan yunkuri. Kwanan nan ne babban bankin kasar watau CBN ya saki
dalolin miliyoyi ga bankuna, hakan ya kawo sa’ida wajen samun dalar.
A wani bangaren kuma, Farfesa Osinbajo ya aikawa Sufeta-Janar na ‘Yan Sanda
Ibrahim K. Idris kira game da yawan satar mutane da ake samu a Najeriya. Kwanan
nan ne aka sace wasu turawa ‘Yan kasar Jamus 2 a cikin Jihar Kaduna.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment