– Hukumar
EFCC ta gano kusan Dala Miliyan 10 a wani gida na Andrew Yakubu
– Tsohon
Manajan NNPC Andrew Yakubu ake zargi ya saci wadannan kudi
– Yanzu haka Kotu ta bada dama Gwamnati ta karbe wannan
kudi
Wani babban Kotun Tarayya da
ke Garin Kano ya bada dama Gwamnatin tarayya ta rike makudan kudin da aka samu
daga gidan Tsohon Manajan Kamfanin main a Najeriya watau NNPC Andrew Yakubu.
Hukumar EFCCta samu wasu
mahaukatan kudi kusan Dala Miliyan 10 a gidan tsohon Manajan Kamfanin NNPC din
na kasa. Andrew Yakubu dai yayi wuf yace duk kyaututtuka ne aka rika kawo masa
lokacin yana Ofis. Yanzu haka Kotu ta bada dama Gwamnati ta karbe wannan kudi.
Alkali mai shari’a Zainab
Abubakar ta bada umarni a mika wadannan makudan kudi da ke hannun EFCC zuwa
Gwamnatin tarayya. Kudin dai sun kai Dala Miliyan 9.8 da kuma wasu Foun £74,000.
Shugaban Hukumar EFCC dai ya
jinjinawa Jami’in da ya bankado wannan kudi watau Adamu Dan Musa a Unguwar
Sabon Tasha da ke Kaduna. Ibrahim Magu ya jinjinawa Ma’aikatan sa da irin
wannan kokari da suka yi.
[NAIJ Hausa]
No comments:
Post a Comment